'Yan bindiga: Sheikh Ahmad Gumi Ya Ja Kunnen Tinubu Kan Maimaita Kuskuren Buhari
- Yayin da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga, Sheikh Ahmed Gumi ya bukaci yin sulhu da ‘yan bindiga a Najeriya
- Gumi ya ce a shirye ya ke ya jagoranci sulhun inda ya bukaci Shugaba Tinubu kada ya yi kuskure irin na gwamnatin Buhari
- Malamin ya shawarci Shugaba Tinubu da ya yi amfani da tsarin da aka bi domin ceto wadanda aka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna – A kokarin ganin an yi sulhu da ‘yan bindiga, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi ya ce a shirye ya ke domin jagorantar sulhun.
Ahmad Abubakar Gumi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya guji yin abin da ya kira kuskure irin na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Gumi ga koka kan kuskuren da Buhari ya yi!
Shehin malamin ya ce Buhari ya tafka kuskure wurin kin amincewa da sulhu da ‘yan bindiga wanda ya kara lalata tsaron kasar, cewar Zagazola Makamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya nuna damuwa kan yadda gwamnatin jihar Kaduna ta ki yin sulhu da ‘yan bindiga yayin da suke ci gaba da sace mutane.
Wannan na zuwa ne bayan ‘yan bindigan sun sace daliban makaranta 287 a wata makaranta da ke karamar hukumar Chikun.
Kusan mako guda kenan da sace daliban amma har zuwa yanzu gwamnatin ba ta iya ceto daliban daga hannun ‘yan bindigar ba.
Shawarar da Gumi ya ba Tinubu kan 'yan bindiga
“A shirye na ke da na jagoranci sulhu tsakanin gwamnati da kuma ‘yan bindiga, wannan aikin addini ne a gare ni domin samun zaman lafiya.”
“Ina fatan Shugaba Tinubu zai amince da sulhu da ‘yan bindiga ba kamar yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi fatali da hakan ba.”
“Ya kamata gwamnati ta yi amfani da tsarin da ta bi yayin sulhu da maharan a harin jirgin kasan hanyar Kaduna zuwa Abuja a 2022.”
- Ahmed Gumi
Ya kuma shawarci gwamnati da ta yi sulhu da ‘yan bindigar domin ceto jama'a da dama baa iya daliban makarantar Kuriga ba kadai, cewar Daily Post.
Gumi ya bukaci sulhu da ‘yan bindiga
Kun ji cewa Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana aniyarsa ta yin sulhu da ‘yan bindiga inda ya nuna amfanin hakan ga tsaron kasar.
Gumi ya bayyana haka ne yayin hira da ‘yan jaridu inda ya ce a shirye ya ke da ya ba da gudunmawa idan Shugaba Tinubu ya bukace shi.
Asali: Legit.ng