Sheikh Gumi Ya Bayyana Bukata da Sharadin Zaman Sulhu Da ’Yan Bindiga

Sheikh Gumi Ya Bayyana Bukata da Sharadin Zaman Sulhu Da ’Yan Bindiga

  • Sheikh Gumi ya bayyana bukatar tattaunawa da ‘yan bindiga domin samar da zaman lafiya a jihohin Najeriya
  • Ya bukaci gwamnati ta samar da hanyoyi tare da shirya wadanda za su tattauna da ‘yan bindigan da suka addabi jama’a
  • Yariman Bakura ya ba da shawarin a tattauna da ‘yan bindiga domin a samu zaman lafiya, musamman a Arewacin Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Najeriya - Shahararren malamin addinin musuluncin nan Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana aniyarsa ta zaman sulhu da ‘yan bindiga domin dawo da zaman lafiya a kasar nan.

A wata hira da yayi da gidan talabijin na TrustTv, Sheikh Gumi ya ce zai shiga tsakani idan har shugaba Bola Tinubu ya bukace shi da ya yi hakan.

Ya kuma bayyana cewa ba dole ya jagoranci zaman sulhun ba, ya kara da cewa zai yi farin ciki ya kasance cikin duk wata tawaga da gwamnati ta amince da ita da ke da alhakin tafiyar da sulhun.

Kara karanta wannan

"Tun Asali Abu 2 Ke Ya Kawo 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya" Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai

Gumi ya ba da sharadin ganawa da 'yan bindiga
Sheikh Ahmad Mahmud Gumi | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Mafita ga yadda za a tattauna da ‘yan bindiga

Ya kuma jaddada bukatar samar da cikakken tsari wanda ya kunshi malamai, sarakuna da malaman jami’o’i da za su hada kai domin ganin an dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya shaidawa gidan talabijin din cewa:

"Ba lallai sai na jagoranta ba, amma zan ba da lokaci na don kasancewa cikinsa. Ba batun shugabanci ba ne; batu ne na cikakken kunshin magance lamarin.”

Ya yi maraba da kiran da tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Sani Yarima ya yi na a tattauna da ‘yan bindiga, inda ya nuna cewa sun cancanci a yi musu afuwa kamar yadda tsaffin tsagerun Neja Delta suka samu dama.

A tun farko, Yarima ya bayyana cewa, talauci ne ya jefa 'yan bindiga aikata irin laifukan da suke aikatawa yanzu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Gwamnatin Jihar APC? Gaskiya Ta Bayyana

An yi daidai da aka nada Ribadu NSA

Sheikh Gumi ya kuma yaba da nadin Nuhu Ribadu a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, kana ya bayyana fatan cewa kada Ribadu ya ba da kunya.

Sheikh Gumi ya bayyana rashin hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro, lamarin da ya ce ya kawo cikas ga yaki da kuncin tsaro a kasar nan.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa game da yiwa manyan jami’an sojoji sama da 100 ritayar dole duba da irin kayayyakin da aka kashe wajen horar da su.

Ya bukaci ‘yan siyasa da su guji siyasantar da harkar sojoji da kuma bangaren shari’a, duba da muhimmancinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.