Matar Aure Ta Fatattaki Kawarta Daga Gidanta Saboda Ta Yaba Kyawun Mijinta

Matar Aure Ta Fatattaki Kawarta Daga Gidanta Saboda Ta Yaba Kyawun Mijinta

  • Wani mutumi ya ba da labarin yadda matarsa ta yanke alaka da kawarta bayan ta yi magana kan kyawun surar da Allah ya yi masa
  • Mutumin ya ce kawar matarsa ta ziyarci gidansu sannan ta fadawa matar tasa cewa yana da kyawu
  • Ya bayar da labarin yadda matarsa ta bukaci ta fice masu daga gida sannan ta goge lambarta tare da yanke duk wata alaka da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matashiyar mata da ta yaba kyawun mijin kawarta ta sha caccaka ba na wasa ba.

Mijin matar, Dr John Bishop, ya ce matar da ake magana a kai ta kawo masu ziyara a gidansu ne.

Matar aure ta yanke alaka da kawarta saboda mijinta
An yin amfan da hotunan don misali ne kawai Hoto: Getty Images/Tim Robberts and Morsa Images.
Asali: Getty Images

Da yake bayar da labarin a shafin X, ya ce tayi magana a kan kyawun da Allah ya yi masa, amma sam hakan bai yiwa matar tasa dadi ba.

Kara karanta wannan

Budurwa ta ce tana samun N4m duk wata daga man ja, bidiyon ya girgiza intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da take daukar matakin gaggawa, matar John ta bukaci kawarta da ta fice mata daga gida sannan ta yanke duk wata alaka da ita.

John ya rubuta:

"Matata ta bani labari game da daya daga cikin kawayenta wacce ta fada mata irin kyawun da nake da shi. Mijinki yana da kyau sosai, ga shi dogo, baki kuma kyakkyawa, kin yi sa'ar samunsa.
"Tambayar da na yi ita ce: "wani amsa kika bata". Madam ta ce kawai ta yi murmushi sannan ta fatattaketa daga gida; ta toshe lambobinta, ta goge su, sannan ta dauki wayata ta tabbata babu lambarta a waya, sannan ta toshe ta a duk shafukan sada zumunta.
"Dariya ta kusa kashe ni yayin da take fada mani abin da ta yi shi ne daidai. Mata ku kare kanku daga masu fuska biyu."

Kara karanta wannan

Dole ma ta hakura: Saurayi ya yi sabani da budurwarsa, ya mata kyautar N1.5m a matsayin neman afuwa

Ga wallafarsa a kasa:

Jama'a sun yi martani kan abin da matar ta yi

@kxesca ta ce:

"Na rasa adadin mutanen da suka fada mani cewa mijina na da kyau. Bai taba zuwa mani a zuciya cewa na toshe su ba. Ina ganin duk muna da yadda mu ke fassara abubuwa. Baya ga haka watakila akwai abin da matashiyar ta fadi, don wannan bai isa a toshe kowa ba."

@Ebyfyn ta ce:

"Babu abin da toshe lambar zai hana. Namijin da zai ci amana zai ci amanarsa."

Kwarto ya halaka mijin matar da yake bibiya

A wani labari na daban, mun ji cewa wani magidanci ya rasa ransa a hannun wani mutum da ya daɗe yana lalata da matarsa ta aure.

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke Ishaya Markus mai shekara 35 da haihuwa bisa laifin kashe marigayi Franchise Albert.

Asali: Legit.ng

Online view pixel