Budurwa Ta Ce Tana Samun N4m Duk Wata Daga Man Ja, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Budurwa Ta Ce Tana Samun N4m Duk Wata Daga Man Ja, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Wata mata da ke zaune a Fatakwal ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya sakamakon ikirarin da ta yi game da sana'arta ta man ja
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, matashiyar ta bayyana cewa tana tashi da Naira miliyan 4 duk wata daga wannan sana'a
  • Yayin da wasu suka gargade ta game da ikirarin da ta yi, wasu sun jinjina mata har da son sanin yadda take wannan sana'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matashiya 'yar Najeriya ta shiga dandalin soshiyal midiya domin baje kolin sana'arta ta man ja.

Matar wacce ke zaune a Port Harcourt tana kasuwancinta ta yada wani bidiyo da ke nuna abubuwa daban-daban da take yi a harkokin kasuwancinta.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da makiyaya ne ke jawo wahalhalun da ake sha a Najeriya, inji fasto Ayodele

Budurwa ta baje kolin kasuwancinta
Ta ce tana samun miliyan 4 duk wata Hoto: @bibireuben
Asali: TikTok

A cikin bidiyonta na TikTok, @bibireuben ta rubuta cewa tana samun Naira miliyan 4 duk wata amma ta yi gum game da sirrin kasuwancin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon @bibireuben ya girgiza TikTok, inda ya haifar da martani da dama daga mutane. Wasu sun ji mata tsoron jefa kanta a matsala da wannan ikirari nata.

Wasu kuma na son sanin yadda take samun wannan ciniki.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon

Fxik ta ce:

"Ina sha'awar kasuwancin daga Enugu ina son sanin karin bayani musamman wadanda zan sayarwa."

iamleviMcCarthy ta ce:

"Ya kamata dai ki sani miyagun mutane na batar da kamanni a matsayin kwastama ki yi tutanin kariyarki."

zeleluxury hair ta ce:

"Don Allah ta yaya zan shiga wannan sana'a domin dai wanda nake yi bai da kan gado."

Kara karanta wannan

Rashin tausayi: 'Yan sanda sun kama wata mata da ta ba diyarta guba

Thilda ta ce:

"Mahaifiyata na yin wannan sana'a kuma matar nan na da kudi faaaa."

Ayinla Olugbenga ya ce:

"Ki rika bar wa kanki sanin abin da kike samu. Ki dunga lura da lamarin tsaro. Shawara ce kawai."

Alvira Anthony ta ce:

"Nuna mani hanya faaaa."

Kazantaccen wurin da ake sarrafa manja

A wani labarin, mun ji cewa jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata matashiya da ke nuna muhallin da take sarrafa man ja.

Bidiyon da aka wallafa a Twitter ya bai mutane mamaki saboda wurin na da datti sosai da tabo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel