Kwarto Ya Halaka Mijin Matar da Yake Lalata da Ita a Adamawa

Kwarto Ya Halaka Mijin Matar da Yake Lalata da Ita a Adamawa

  • Wani magidanci ya rasa ransa a jihar Adamawa a hannun kwarton da yake lalata da matarsa bayan faɗa ya ɓarke tsakaninsu
  • Wanda ake zargin dai ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na halaka mijin matar da ya daɗe yana lalata da ita
  • Ƴan sanda sun tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala gudanar da bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Wani magidanci ya rasa ransa a hannun wani mutum da ya daɗe yana lalata da matarsa ta aure.

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke Ishaya Markus mai shekara 35 da haihuwa bisa laifin kashe marigayi Franchise Albert, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

"Mijina ya daina kwana da ni a gado" Matar aure ta cire kunya ta fashe da kuka a kotu

Kwarto ya halaka magidanci a Adamawa
Kwarto salwantar da ran magidanci a Adamawa Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Arangamar da ta kai ga mutuwar Albert ta faru ne a ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Fufore inda Franchise da matarsa ​​Libyatu ƴar shekara 20 ke zaune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Majiyoyin da suka san ma'auratan sun ce sun fara samun matsala ne tun shekarar 2022 lokacin da Libiyatu ta fara hulɗa da Markus.

An ce Albert ya gargaɗi matarsa ​​da wanda ake zargin da su daina ganin juna amma sun yi kunnen uwar shegu.

Libyatu ta gayawa ƴan sanda cewa:

"Mijina ya gargaɗe mu lokacin da ya gano abin da muke yi. Da ni da shi mun yi faɗa kan lamarin wanda hakan ya sanya na tafi gidan iyayena.
“Ishaya (Markus) ya biyo ni can inda ya kai ni daji ya yi lalata da ni har sau biyar."

Tace ko bayan da suka sasanta da mijinta ta koma daƙinta, Markus ya ci gaba da bibiyarta har zuwa lokacin da ƙazamin faɗa ya ɓarke tsakaninsa da mijinta.

Kara karanta wannan

"Ya kashe sama da N30m": Magidanci ya shiga damuwa da matarsa da ya kai Turai ta nuna halinta

A nasa ɓangaren, Markus ya amsa cewa yana lalata da matar Franchise tare da halaka shi a yayin faɗan da suka yi, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Dankombo Morris, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za a gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Matar aure ta koka kan mijinta a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi ƙaramin wasan kwaikwayo a kotun yanki da ke Centre-Igboro, Ilorin, babban birnin jihar Kwara lokacin da wata matar aure, Aminat Nagode-Allah ta fashe da kuka.

Matar dai ta fashe kuka a gaban alƙali yayin da take ƙorafin mijinta ya ƙaurace ma gadon aurensu na Sunnah

Asali: Legit.ng

Online view pixel