Tinubu Ya Ba Gwamnonin Jihohi Sabon Umarni Kan Mafi Karancin Albashi, Bayanai Sun Fito
- Yayin da ake cikin matsi a Najeriya, Shugaba Bola Tinubu ya bukaci gwamnoni kan fara biyan kudaden rage radadi
- Tinubu ya ce idan da ana biyan kudaden, tabbas za a rage yawan tashin farashin kayayyaki a fadin kasar baki daya
- Legit Hausa ta ji ta bakin hadimin Gwamna Inuwa na jihar Gombe, Yusuf Alyusra kan biyan kudade rage radadin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi su fara biyan kudaden rage radadi kafin aiwatar da sabon mafi karancin albashi.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin kaddamar da wani aiki a Minna da ke jihar Neja a yau Litinin 11 ga watan Maris.
Menene Tinubu ke cewa kan halin kunci?
Shugaban ya ce hakan ya zama dole ganin yadda 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya ce idan da gwamnonin su na biyan wadannan kudaden, da an rage matsaloli da kuma tashin farashin kaya.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ta korafi kan halin yunwa da ake ciki saboda wasu tsare-tsaren tattalin arziki a wannan gwamnati.
Rokon da Tinubu ya yi ga gwamnoni
"Idan da kuna biyan kudaden rage radadi kafin aiwatar da mafi karancin albashi zai rage wahalar da ake sha."
"Ya kamata dukkan gwamnoni su fara biyan kudaden, idan suka hada da abin da suke samu zai rage musu wahala."
"Ina rokonku, ba wai umarni na ke baku ba, ina rokon jihohi da su fara biyan kudaden domin rage radadin da ake ciki na cire tallafin mai."
- Bola Tinubu
Tinubu ya ce biyan kudin zai yi matukar tasiri wurin dakile tashin farashin kayayyaki a kasar, cewar Politics Nigeria.
Legit Hausa ta ji ta bakin hadimin Gwamna Inuwa na jihar Gombe kan biyan kudade rage radadin.
Yusuf Alyusra ya tabbatarwa wakilin Legit Hausa cewa Gwamna Inuwa ya na ci gaba da biyan kudaden.
Ya ce:
"Tun da Gwamna Inuwa ya fara biyan kudi N10,000 har yau ba a tsaya ba, babu wata daya da ba a ba da kudin ba har zuwa yau."
"Zuwa yanzu an ba da kudin ya kai watanni uku zuwa huɗu har wannan watan da ya wuce ma an biya."
Ajuri ya zargi Emefiele ya lalata gwamnatin Buhari
Kun ji cewa hadimin shugaban kasa, Bola Tinubu, Ajuri Ngelale ya bayyana irin badakalar da tsohon gwamnan babban bankin CBN, ya yi.
Ajuri ya ce Emefiele ya kwashe biliyoyin daloli domin aiwatar da wasu ayyuka ba tare da sanin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.
Asali: Legit.ng