Ramadan: Tinubu Ya Aika Muhimmin Sako Ga Masu Hali Yayin da Aka Fara Azumi

Ramadan: Tinubu Ya Aika Muhimmin Sako Ga Masu Hali Yayin da Aka Fara Azumi

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci masu hannu da shuni da su taimaki talakawa musamman a lokacin azumin watan Ramadan
  • Shugaba Tinubu ya faɗi hakan ne a wajen rabon tallafin shinkafa da Sanata Abdul'aziz Yari ya ƙaddamar a Kano
  • Shugaban ƙasar wanda ya samu wakilci a wajen taron ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su yi addu'o'in samun zaman lafiya a lokacin azumi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci masu hannu da shuni da su taimaka wa marasa galihu a cikin al’umma domin rage musu raɗaɗi musamman a lokacin azumin Ramadan.

Bola Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Kano a lokacin da yake ƙaddamar da rabon manyan motoci 140 na shinkafa da Sanata Abdullahi Yari ya bayar domin karrama shugaban ƙasan, cewar rahoton jaridar Premium Times.

Kara karanta wannan

Shettima ya fadi babban tanadin da Shugaba Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya

Tinubu ya shawarci masu hannu da shuni
Tinubu ya bukaci masu arziki su taimaki talakawa Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya shawarci ƴan Najeriya

Shugaba Tinubu wanda ya samu wakilcin babban mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya yabawa wannan karamcin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an yi hakan ne domin tallafa wa mutanen da ke cikin mawuyacin hali a wannan mawuyacin lokacin da ake ciki a ƙasar nan.

A kalamansa:

"A duk faɗin duniya, jagoranci na mutum fiye da ɗaya ne. A ko da yaushe akwai buƙatar a taimaka wa marasa ƙarfi a cikin al'umma.
"Mu taru mu haɗa kai a matsayin ƙasa, mu samar da ingantacciyar Najeriya."

- Abdulaziz Abdulaziz

Tinubu ya yabawa Yari bisa bayar da gudunmawar tireloli 140 na shinkafa da aka sanya sunansa da hotonsa domin rabawa ga marasa galihu.

Ya kuma ce, kayayyakin za su taimaka sosai wajen sauƙaƙa wahalhalun da mutane da dama ke fuskanta a wannan lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya tuna da talakawa, ya rage farashin kayan hatsi saboda azumi

Shugaban, ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su yi addu’ar samun haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban ƙasar nan a cikin watan Ramadan, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Yari zai raba buhuna 84,000 na shinkafa

Tun da farko, wakilin Sanata Yari, Abubakar Danburam, ya ce manyan motocin 140 na dauke da buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 84,000.

Alhaji Danburam ya bayyana cewa za a raba shinkafar ga aƙalla gidaje 500,000 a yankin Arewacin Najeriya.

Ya ce wannan shirin an fito da shi ne domin taimakawa ƙoƙarin da Shugaba Tinubu yake yi na rage raɗaɗi ga marasa galihu a cikin al'umma.

Gwamna Radda ya karya farashi saboda azumi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sauke farashin kayan hatsi domin azumin watan Ramadan.

Gwamnan ya ƙaddamar da shirin sayar da kayan hatsi irinsu masara, gero da dawa kan farashin N20,000 duk buhu domin sauƙaƙawa al'ummar jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel