A Karon Farko Buhari Ya Fadi Gaskiyar Yadda Yake Kallon Salon Mulkin Shugaba Tinubu

A Karon Farko Buhari Ya Fadi Gaskiyar Yadda Yake Kallon Salon Mulkin Shugaba Tinubu

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu babban yabo daga magabacinsa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Buhari ya yi nuni da cewa shugaban ƙasan yana iyakar bakin ƙoƙarinsa duk kuwa da ƙorafe-ƙorafen da ƴan Najeriya ke yi na halin matsin tattalin arziƙi
  • Tsohon shugaban ƙasan ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara sanya juriya domin Tinubu zai fitar da ƙasar nan daga halin da take ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yabi salon rikon Mai girma Bola Tinubu bayan hawansa mulki.

Yabon na Shugaba Tinubu na zuwa ne duk da halin taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ƴan Najeriya ke fuskanta a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Ramadan: Tinubu ya aika muhimmin sako ga masu hali yayin da aka fara azumi

Buhari ya yabi Shugaba Tinubu
Tinubu ya samu yabo daga Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

A cewar Buhari, babu wani abin da wani zai iya yi don taimakawa ƙasar a halin yanzu yayin da yake nuni da cewa Najeriya tana da “sarƙaƙiya sosai”, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin matsin tattalin arziƙi dai ya yi sama tun bayan lokacin da Buhari ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Me Buhari ya ce kan mulkin Tinubu?

Sai dai da yake magana a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar kwastam da jami’an hukumar kwastam ta Najeriya a garin Daura na jihar Katsina, Buhari ya ce mulkin Najeriya aiki ne mai wahala ga kowa.

Ya roki ƴan Najeriya da su jure wa matsalolin tattalin arziƙin da ake fama da su a ƙasar nan tare da marawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati mai ci a yanzu baya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na amfani da kasafin kudi iri 2 a 2024? Fadar shugaban kasa ta fadi gaskiya

Jaridar The Punch ta ambato tsohon shugaban ƙasar na cewa:

"Na gode ƙwarai da zuwan ku. Na yaba sosai. Ina tunanin Tinubu ya yi ƙoƙari sosai.
"Najeriya tana da sarƙaƙiya sosai. Haƙiƙa, babu abin da wani zai iya yi."

Majalisa ta fara binciken gwamnatin Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta umarci kwamitinta ya gudanar da bincike kan yadda aka kashe kuɗaɗen ƙidayar shekarar 2023 har N200bn.

An dai kashe kuɗaɗen ne a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda Tinubu ya gaji mulki a hannunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng