Ramadan: Muhimman Abubuwa 10 da Suka Dace Musulmi Ya Kauce Masu a Wata Mai Albarka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A yau Litinin ce 11 ga watan Maris aka fara azumin watan Ramadana bayan sanar da ganin wata a daren jiya Lahadi 10 ga watan Maris.
Watan Ramadan shi ne mafi alherin sauran watanni da ake da su a Musulunci inda mutane ke komawa ga Ubangijinsu wurin yin ibadu.
Abubuwan da ba a zo da azumin Ramadan
Azumi a wannan wata ya zam a wajibi ga dukkan baligi sai dai idan akwai rashin lafiya ko halin tafiya da sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta jero muku abubuwan da ya kamata Musulmai su kauce musu a wannan wata.
1. Cin abinci ko shan wani abu da azumi
Dole kowane Musulmi ya kiyaye duk wani abin da ya shafi ci ko shan wani abu tun daga lokacin suhur har lokacin buda baki.
Ci ko shan wani abu da gangan ya na karya azumi sai dai idan da kuskure aka yi, cewar Morocco World News.
2. Shan taba ko kayan maye
A Musulunci hakan ya haramta ko da ba a lokacin azumi ba domin yana kawar da hankalin dan Adam.
Shan taba ko shisha, giya ko wiwi da sauran kayan maye na karya azumi nan take bayan zunubi da mutum zai samu.
3. Saduwa
Ma'aurata dole su guji duk wani alaka da zai jawo su ji dadi da juna musamman a lokacin da ake azumi.
Aikata hakan babban laifi ne wanda ke jawo fushin Allah kan wadanda suka aikata haka, cewar rahoton Vanguard.
4. Gulma
Yawan yin gulma da makamantansu sun haramta ko da ba a lokacin azumi, yin hakan babban laifi ne.
A watan azumi aikata irin wadannan na jawo rauni a azumin Musulmi wanda hakan ya zama dole a kauce masa.
5. Musu da hayaniya ko gaba
Watan Ramadan lokaci ne na yafiya da kuma zaman lafiya a tsakanin mutane a ko da yaushe, Premium Times ta fitar da wannan.
Shiga cikin musu da gaba da wani ko kuma cece-kuce babu dalili ya na kawo rauni ga azumin mutum.
6. Shagala
Dole ne kowane Musulmi ya kaucewa shagala da za ta hana shi mai da hankali kan bautar ubangji.
A koda yaushe ana son Musulmi ya shagaltu da karatun Alqur'ani da ambaton Allah da kyaututtuka.
7. Wasa da ibada
Dole ne kowane Musulmi ya kula da Sallah matuka da sauran ibadu saboda su ne ginshikin samun albarkar wannan wata.
Wasa da Ibada ya na matukar kawo cikas da rauni a azumin mutum wanda ya wuni ya na cikin yunwa da ƙishirwa.
8. Bata lokaci
Mafi yawan mutane su kan bata lokacinsu wurin aikata wasu abubuwa da suke shagaltar da su bautar Allah.
A wannan wata ana bukatar Musulmai su kasance kowane lokaci su na karatun Alkur'ani da kuma ambaton Allah.
9. Cin abinci da yawa
Ana bukatar Musulmi ya daidaita yawan cin abinci ko shan ruwa ba tare da ya yi yawa ko almubazzaranci ya shiga ba.
Dole kowane Musulmi ya kula da irin abincin da ya kamata ya rinka ci ko sha musamman a wannan wata da ba za su kawo masa matsala ba.
10. Rashin yin kyauta
Wannan wata ne na alfarma da ke buƙatar yin kyauta musamman ga marasa karfi domin samun albarka watan.
Rashin yin kyaututtuka matsala ne musamman ga wadanda suke da abin hannu da kuma halin da ake ciki.
An ga watan Ramadan
Kun ji cewa Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan Ramadana domin fara azumi a yau Litinin 11 ga watan Maris.
Sultan ya bayyana ganin watan ne a daren jiya Lahadi 10 ga watan Maris bayan tabbatar da ganin watan a wasu wurare.
Asali: Legit.ng