Ramadan: Farashin Kayan Abinci a Abuja Sun Yi Tashin Gwauron Zabi
- A yayin da Musulmi suka fara azumin watan Ramadan na bana, farashin kayan abinci a Abuja ya yi tashin gwauron zabi da kusan kaso 95
- Wani bincike ya nuna cewa farashin kayan abinci irin su shinkafa, wake, dawa, garri da masara suna neman nunka farashinsu a yau
- A bangaren kayan hada miya irin su manja, man gyada, fakitin maggi da na gishiri su ma sun kara kudi, lamarin da ya saka mutane yin korafi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - A yayin da Musulmai suka fara azumin watan Ramadan na bana, farashin kayan abinci a Abuja ya karu da kashi 95 cikin 100.
Jaridar Daily Trust da ta ziyarci babbar kasuwar Abaji a ranar Asabar, ta lura cewa farashin kayan abinci irin su shinkafa, wake, dawa, garri da masara sun yi tashin gwauron zabi.
Karin kudin da aka samu a abinci
Binciken da jaridar ta yi, ya nuna cewa mudu na shinkafa da aka sayar a mako guda da ya gabata, kan N1,800 yanzu ana sayar da a kan N2,000 kan kowane mudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da mudu na wake da aka sayar a kan N1,400 a makon da ya gabata a kasuwar, yanzu ana sayar da shi N1,600 kan kowane mudu.
A makon da ya gabata, doya guda daya an sayar da ita a kan N1,000 amma yanzu ana sayar da ita a kan N1,300, yayin da ake sayar da mudun garin dawa a kan 1,200.
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa kayan hada miya irin su manja, man gyada, fakitin maggi da na gishiri su ma sun kara kudi da kashi 95 a kasuwar.
Mazauna Abuja sun koka da tsadar abinci
Wasu mazauna Abuja sun koka kan yadda ake samun karuwar kudin kayan abinci da kayan masarufi a kasuwa gabanin azumin watan Ramadan a yankin.
“Abin takaici ne yadda wasu ‘yan kasuwa suke yin amfani da watan Ramadan wajen kara kudin kayansu, musamman kayan abinci wanda hakan ba shi da kyau.”
- In ji wata mai sayen kaya a kasuwar, Zuwaira Adamu.
Wani mai sayan kayan abinci a kasuwar, Usman Yakubu, ya dora laifin karuwar kudin kayan a kan rashin daukar mataki da shugaban kasuwar yankin ya yi.
Wannan na zuwa duk da Vanguard ta ruwaito cewa 'yan kasuwa sun yi alkawarin daidaita farashin kayan a lokacin azumi.
Ramadan: Sakon Tinubu ga attajiran Najeriya
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa an yi kira ga masu hannu da shuni a Najeriya da su dauki nauyin taimakawa marasa galihu a cikin watan Ramadan.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya yi wannan roko, inda ya bayyana cewa masu rauni na bukatar taimako a kasar.
Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin irin wadannan ayyuka wajen taimaka wa mutanen da ke fuskantar matsala a wannan mawuyacin lokaci.
Asali: Legit.ng