Faduwar Naira Ta Jawo Kudin Sauke Fetur Ya Haura Zuwa N1400, an Gano Illolin da Hakan Zai Haifar

Faduwar Naira Ta Jawo Kudin Sauke Fetur Ya Haura Zuwa N1400, an Gano Illolin da Hakan Zai Haifar

  • An ruwaito cewa sabon kudin sauke man fetur a yanzu ya haura N1,400 a kan kowace lita sakamakon faduwar darajar Naira
  • A yanzu kudin Najeriya a kasuwanin hada-hada na gwamnati da ma na bayan fage ya haura N1,600 akan kowace dalar Amurka 1
  • Hakan na nufin dole gwamnatin Najeriya ta kara himma wajen ganin farashin man fetur din ya daidaita kan N600 ga kowace lita

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Akwai fargabar cewa nan gaba kadan gwamnatin tarayya za ta sake duba matsayarta kan daidaita farashin man fetur yayin da kudin kasar ya sake faduwa.

Sakamakon karuwar kudin sauke man fetur da a yanzu ya haura N1,400, masana na ganin cewa ba lallai ne gwamnati ta ci gaba da sayar da litar fetur din akan N600 ba.

Kara karanta wannan

N11,000/50kg: Hauhawar farashin siminti da matsalolin da yake haifarwa a Najeriya

Kamfanin NNPC
Bayanai sun nuna cewa har yanzu ana biyan tallafin man fetur. Hoto: NNPC Limited, Nurphoto
Asali: Getty Images

Wani bincike da jaridar The Sun ta yi ya nuna cewa kudin da ake kashewa wajen hidimar sauke man fetur ya karu zuwa Naira 1,424 kan kowace lita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu karin N856 na kudin

Wannan kuwa ya hada da farashin fetur din a kasar waje, sufurin man, inshora, da sauran kudaden da ake kashewa wajen sauke shi.

Hakan na nufin an samu karin N856 a kan N568 da kamfanin NNPC ke sayar da kowace lita a gidajen sayar da mansa da ke a fadin kasar.

Wannan na zuwa kasa da wata daya bayan da Business Day ta ruwaito cewa farashin sauke fetur din ya haura zuwa N1000 kan kowace lita.

Gwamnati na biyan tallafin fetur - IMF

A watan Fabrairun 2024, hukumar ba da lamuni ta duniya (IMF) ta zargi gwamnatin Najeriya da dawo da biyan tallafin mai ta bayan fage.

Kara karanta wannan

CBN ya dauki mataki mai karfi domin farfado da darajar Naira a kan Dalar Amurka

A wani martani, manajan kamfanin NNPCL, Malam Mele Kyari, ya tabbatar da cewa gwamnati ba ta biyan tallafin man.

A cewarsa:

"Babu wani tallafi da muke biya. Yanzu haka muna caske kudadenmu daga duk wani fetur da muke shigo da shi muka sayarwa 'yan kasuwa, ba batun biyan tallafi."

Tallafin fetur: Tsohon gwamna ya magantu

Legit Hausa ta kawo maku rahoto kan ikirarin tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda da shi ma ya jaddada cewa har yanzu gwamnatin na biyan tallafin fetur.

Amma a mahangar Yuguda, gwamnati ta toshe hanyar da wasu tsirarun 'yan kasar ke karkatar da kudin tallafin, tare da mayar da hankali wajen dakile farashin fetur din daga tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel