Kashim Shettima Ya Fadi Abu 1 da Za a Yi Don Magance Matsalar Tsaro a Najeriya

Kashim Shettima Ya Fadi Abu 1 da Za a Yi Don Magance Matsalar Tsaro a Najeriya

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi magana kan matsalar tsaro da ake fuskanta a ƙasar nan
  • Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa idan ana son ganin an kawo ƙarshen matsalar dole ne sai an tabbatar da tsaro a iyakokin ƙasar nan
  • Ya koka kan yadda ake ƙara samun ƙwararar makamai cikin ƙasar nan saboda rashin kyakkyawan tsaro a iyakokin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jaddada bukatar magance matsalar rashin tsaro a kan iyakokin ƙasar domin samun damar magance matsalar tsaro da al'ummar ƙasar nan ke fuskanta.

Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da tawagar hukumar raya al’ummomin kan iyakokin ƙasa (BCDA), ƙarƙashin jagorancin babban sakatarenta, Junaid Abdullahi, a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gamu da sabuwar matsala, ASUU zata sa kafar wando ɗaya da FG kan muhimmin abu 1

Kashim Shettima ya yi magana kan rashin tsaro
Kashim Shettima ya gano mafita kan rashin tsarp a Najeriya Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana rawar da hukumar ke takawa wajen sauya fasalin al’umma da yanayin tsaro na kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban ƙasan, ya yi alƙawarin cewa gwamnatin tarayya za ta ɗauki matakai don tabbatar da ci gaban al'ummomin kan iyakokin Najeriya don inganta rayuwar mazauna yankin da kuma yanayin tsaro a ƙasar nan.

A cewar wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban ƙasan kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Stanley Nkwocha, ya fitar, ya lura da ƙalubalen da waɗannan al’ummomi ke fuskanta da suka haɗa da rashin tsaro da rashin ababen more rayuwa.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Rashin kyakkyawan tsaro a kan iyakokinmu a bayyane yake kan yadda ƙananan makamai ke ƙwararowa. Muna buƙatar mu duba rawar da BCDA ke takawa domin magance matsalar tsaro a ƙasarmu."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Babban malamin addini ya tura sako mai muhimmanci ga Shugaba Tinubu

Ya jaddada mahimmancin al'ummomin kan iyaka a cikin tsaron kasa tare da yin alkawarin ci gaba da tallafawa buƙatun ci gaban su.

Gwamnati Za Ta Samar da Dakarun Noma

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shirya samar da dakarun noma domin magance ƙalubalen ƴan bindiga da manoma ke fuskanta.

Majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) ƙarƙashin jagorancin Kashim Shettima, ita ce ta sanar da hakan don magance ƙarancin abinci, tsadar abinci, yunwa da rage matsin tattalin arziƙi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel