Kiran Juyin Mulki: Minista Ya Dauki Zafi, Ya Bada Umarni Ga Jami'an Tsaro a Dauki Mataki
- Yayin da wasu 'yan Najeriya ke ci gaba da kiran a yi juyin mulki, Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya tura gargadi
- Matawalle ya bayyana cewa masu fatan kifar da Gwamnatin Bola Tinubu a matsayin marasa kishin kasa da dimukradiyya
- Ministan ya umarci hukumar tsaro da DIA da su dauki mataki mai tsauri kan masu kiran kifar da Gwamnatin farar hula
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi gargadi kan masu fatan juyin mulki a Najeriya.
Bello Matawalle ya umarci hukumar tsaro ta DIA da su fara farautar duk masu kiran a kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Wani gargadi aka yi wa 'yan dadi juyin mulki?
Ministan ya bayyana haka ne ta bakin daraktan yada labaran ma'aikatar tsaro, Henshaw Ogubike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana masu fatan juyin mulki da mugaye wadanda basu son ci gaban dimukradiyya a Najeriya.
Ya kuma tura musu sakon gargadi da cewa idan aka cafke su ba za su ji ta dadi ba domin za su fuskanci hukunci.
Juyin mulki: Matawalle ya ce babu kishin kasa
"Kiran kifar da gwamnatin farar hula abin takaici ne da rashin kishin kasa, sojoji sun amince da dimukradiyya kuma za su ci gaba da kare martabarta."
"Dukkan masu kiran kifar da gwamnati su yi gaggawar janyewa su fuskanci ci gaban da dimukradiyya ta kawo a kasar."
"Rundunar sojin kasar ta himmatu wurin tabbatar da dorewar dimukradiyya inda ta samu alaƙa mai ƙarfi tsakaninta da fararen hula."
- Bello Matawalle
Ministan har ila yau, ya bukaci 'yan kasar da su goyi bayan Shugaba Tinubu a kokarinsa na kawo karshen matsalolin kasar.
Sojoji sun gargadi masu kiran kifar da Tinubu
A baya, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi gargadi kan masu kiran a kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Sojojin sun bayyana masu irin wannan halayyar da cewa basu da kishin kasa inda ta ce za su fuskanci hukunci.
Wannan na zuwa ne bayan wasu 'yan Najeriya na kiraye-kirayen a gudanar da juyin mulki.
Asali: Legit.ng