Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta a Sansanin Ƴan Bindiga a Jihohin Arewa, Sun Kashe da Yawa

Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta a Sansanin Ƴan Bindiga a Jihohin Arewa, Sun Kashe da Yawa

  • Jirgin rundunar sojin sama ya halaka ƴan bindiga masu yawa yayin da ya kai samame maɓoyar manyan ƴan ta'adda biyu a Zamfara da Katsina
  • Mai magana da yawun NAF, AVM Edward Gabkwet, ya ce sojojin sun samu nasarori a farmakin da suka kai ranakun Talata da Laraba
  • Ya ce har yanzun babu tabbacin ko an kashe manyan ƴan bindigan biyu, Maudi Maudi da Alhaji Na-Shama, a hare-haren lokuta daban-daban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rundunar sojin saman Najeriya ta ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kai samame ta sama kan wasu manyan ‘yan bindiga biyu a jihohin Katsina da Zamfara.

Sojojin saman sun kai samamen farko ne ranar Talata kan sansanin ƙasurgumin ɗan bindiga, Maudi Maudi a kudancin kauyen Tsaskiya, ƙaramar hukumar Safana a Katsina.

Kara karanta wannan

Jirgin rundunar sojin saman Najeriya ya gamu da hatsari a Kaduna, bayanai sun fito

NAF ta kashe adadi mai yawa na yan bindiga a Zamfara da Katsina.
Sojojin Saman Najeriya Sun Halaka Ƴan Bindiga Da Yawa a Jihohin Zamfara da Katsina Hoto: Nigeria Air force HQ
Asali: Facebook

Mai magana da yawun rundunar NAF, AVM Edward Gabkwet, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce babu tabbacin ko Maudi Maudi ya mutu a ruwan wutan da sojojin suka masa amma da yawa daga cikin mambobin tawagarsa sun baƙunci lahira.

Gabkwet ya ce a bayanan da aka tattara bayan samamen, an gano cewa sansanin ƴan bindigan ya ƙone yayin da wasu tsiraru daga cikin ƴan bindigan suka tsira.

Ya ce:

"Duk da an kashe ƴan bindiga da yawa a farmakin amma babu tabbacin ko shugabansu, Maudi Maudi, na cikin waɗanda aka tura lahira."

Wane nasarori NAF ta samu a jihar Zamfara?

Kakakin NAF ya ƙara da cewa dakarun sojin saman sun kai makamancin irin wannan farmaki ranar Laraba kan hatsabibin ɗan bindiga, Alhaji Na-Shama a Zamfara.

Kara karanta wannan

Majalisa ta buƙaci Shugaba Tinubu ya gaggauta kawo ƙarshen ƴan bindiga a Jihar Arewa

A cewarsa, sojojin sun yi ruwan bama-bamai ta sama kan mafakar kasurgumin ɗan bindigar da ke ƙauyen Ussu, yankin Nasarawar Mailayi a ƙaramar hukumar Birnin Magaji.

A rahoton Leadership, an ji sahihan bayanan sirri da mutane suka tattara sun tabbatar da kashe wasu makusantan Na-Shama da kuma rusa sansaninsa gaba daya da kayan aikinsa.

A cewarsa, har yanzu ba a tabbatar da ko Na-Shama na cikin wadanda aka kashe ba, inda ya ƙara da cewa farmakin sama yana taimakawa wajen kare rayukan fararen hula da kuma lalata sansanonin 'yan ta'adda.

Ƴan bindiga sun tafka ta'adi a Benue

A wani rahoton kuma Wasu ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai mummunan hari a kauyen Azandeh a karamar hukumar Ukum ta jihar Benuwai.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kashe mutane da yawa cikin har ƴan uwan juna su 7, sun ƙona gidaje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262