Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makaranta, Sun Dauke Yaran Firamare
- Tsagerun 'yan bindiga sun kai hari makarantar firmare ta LEA, a garin Kuriga, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
- An rahoto cewa maharan sun yi harbe-harbe tare da sace dalibai da ake tunanin yawansu ya kai 100 a harin
- Haka kuma, shugabar makarantar da wasu ma'aikata suna cikin wadanda 'yan bindigar suka tasa keyarsu zuwa cikin jeji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
An samu tashin hankali a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, lokacin da wasu 'yan bindiga suka farmaki makarantar firmare ta LEA, Kuriga (1) tare da sace dalibai da dama.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, ba a san adadin daliban da aka sace ba zuwa yanzu, amma mazauna yankin sun ce sun kai kimanin su 100.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa shugaban malamai na makarantar da wasu ma'aikata suna daga cikin wadanda aka sace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta'adin 'Yan bindiga a Kaduna
An kuma tattaro cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 8:20 na safiya, jim kadan bayan bude makarantar a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.
Makarantar sakandaren ta koma cikin garin Kuriga 'yan shekaru da suka gabata saboda rashin tsaro, inda suka bar tsohon gininsu da ke wajen garin.
Mazauna Kaduna sun yi tsokaci
Wani mazaunin yankin, Shittu ya tabbatar da faruwar lamarin, cewa yawancin daliban sun tsere daga ajujuwansu yayin da suka hango 'yan bindigar a harabar makarantar.
Wani Lawal Kuriga ma ya tabbatar da cewa an tasa keyar mutanen da aka sace zuwa cikin jeji.
Babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar kasancewar kwamishinan ma'aikatar tsaron jihar, Samuel Aruwan, bai amsa sakon da aka tura masa ba zuwa yanzu.
Haka kuma, ba a samu jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ba, bai amsa sakon da aka tura masa ba.
An sace mutum 60 a Zamfara
A wani labarin kuma, mun ji cewa an yi awon gaba da dimbin mutane sakamakon mummunan harin da tsagerun yan bindiga suka kai a garin Rimi, a karamar hukumar Bakura jihar Zamfara, ranar Juma'a.
Kwamishanan labaran jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya tabbatar da hakan ranar Juma'a. A cewarsa, an yi garkuwa da kimanin mutum 60 amma jami'an tsaro basu tabbatar da adadin ba.
Asali: Legit.ng