Bayan Kyautar Pantami, Gwamna da NAHCON Sun Gwangwaje 'Yar Musabaka da Kyaututtuka

Bayan Kyautar Pantami, Gwamna da NAHCON Sun Gwangwaje 'Yar Musabaka da Kyaututtuka

  • Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya ba daliba Hajara Ibrahim Dan'azumi kyautar Naira miliyan biyar
  • Har ila yau, hukumar Alhazai ta kasa ta gwangwaje dalibar da kyautar kujerar hajji da za a yi a bana
  • Legit Hausa ta ji ta bakin Hajara Ibrahim kan kyaututtukan da ta samu bayan samun nasara a gasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya gwangwaje daliba Hajara Ibrahim Dan'azumi da kyautar kudi.

Gwamna ya bai wa dalibar kyautar kudi har naira miliyan biyar saboda kokarinta a gasar musabaka ta duniya.

Hajara ta samu kyaututtuka daga Gwamna Inuwa da hukumar NAHCON
Dalibar ta samu kyaututtukan ne bayan lashe gasar musabaka ta duniya. Hoto: Inuwa Yahaya, Hajara Ibrahim Dan'azumi.
Asali: Facebook

Wace irin kyauta gwamnan ya yi wa Hajara?

Kara karanta wannan

Kungiyar Izala ta yi martani kan hallaka malamin musulunci, ta tura sakon gargadi

Har ila yau, gwamna ya bai wa makarantar islamiyya da Hajara ta ke kyautar miliyan biyar don inganta harkokinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, Hajara ta lashe gasar musabaka ta duniya da aka gudanar a kasar Jordan a watan Faburairu.

Daga bisani hukumar Alhazai ta gwangwaje dalibar da kyautar kujerar hajji da za a yi gudanar a bana.

Hajara ta wakilci Najeriya inda ta zama zakara a tsakanin sauran ‘yan takara daga ƙasashe 39 a gasar Izu 60 tare da Tajwidi a gasar ta duniya karo na 18 ta mata a Jordan.

Martanin gwamnan kan nasarar Hajara

Tun farko gwamnan ya taya Hajara murnar lashe gasar da aka gudanar a Jordan inda ya ce suna alfahari da ita.

Gwamna ya bayyana haka ne ta bakin sakataren yada labaransa, Isma'ila Uba Misilli a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar na ba da tallafin naira 100,000? An bankado shirin wasu mazambata

Gwamnan ya nuna jin dadinsa kan nasarar inda ya ce tabbas hakan zai karawa sauran ɗalibai himma a wurin karatu.

Martanin Hajara kan kyaututtukan

Legit Hausa ta ji ta bakin Hajara Ibrahim kan kyaututtukan da ta samu bayan samun nasara a gasar.

Hajara ta godewa mai girman gwamnan da kuma Hukumar NAHCON kan kyaututtukan da suka bata.

"Ina mika sakon godiya ga mai girma Gwamna Inuwa Yahaya, ubangiji ya saka masa da alkairi da wannan kyauta ya kuma masa jagora a cikin mulkinsa."

- Hajara

Pantami ya ba Hajara kyautar mota

Kun ji cewa, tsohon Ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Pantami ya gwangwaje daliba Hajara Ibrahim Dan'azumi da kyautar mota.

Pantami bayan ya ba ta kyautar mota ya kuma yi alkawarin biya mata kudin makarantar har ta karasa.

Wannan na zuwa ne bayan Hajara ta lashe gasar musabaka da aka yi ta duniya a ƙasar Jordan a watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.