Pantami Ya Gwangwaje Dalibar da Ta Lashe Gasar Musabaka da Manyan Kyaututtuka 2, Ta Yi Martani

Pantami Ya Gwangwaje Dalibar da Ta Lashe Gasar Musabaka da Manyan Kyaututtuka 2, Ta Yi Martani

  • Yayin da daliba 'yar asalin jihar Gombe ta samu nasarar lashe gasar musabaka ta duniya, Pantami ya gwangwaje ta da kyauta
  • Tsohon Ministan ya bai wa Hajara Ibrahim Dan'azumi kyautar mota da kuma tallafin karatu har ta kammala tun da ta riga ta fara
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Inuwa Yahaya ya yi alkawarin ganawa Hajara da zarar ya dawo daga tafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya gwangwaje dalibar da ta yi nasara a gasar musabaka ta duniya da kyaututtuka.

Pantami ya bai wa dalibar mai suna Hajara Ibrahim Dan'azumi kyautar mota da kuma tallafin karatu har ta kammala.

Kara karanta wannan

Kamfanin Ajaokuta: Majalisa za ta binciki gwamnatin Yar'adua, Jonathan da Buhari kan fitar da $496m

Tsohon Minista ya bai wa dalibar manyan kyaututtuka bayan nasarar lashe gasar musabaka a Jordan
Pantami ya bai wa Hajara kyautar ce bayan ya gana da su a Gombe. Hoto: Isa Ibrahim Pantami, Hajara Ibrahim Dan'azumi.
Asali: Facebook

Menene dalilin zuwan Pantami Gombe?

Hakan ya biyo bayan ziyarar da ya kai jihar Gombe don kaddamar da bude makaranta a Unguwar Pantami da ke birnin Gombe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da Legit Hausa ta tambayi Hajara gaskiyar wannan kyauta, ta tabbatar da hakan inda ta yi godiya tare da sanya albarka.

Ta kuma tabbatar da cewa Gwamna Inuwa ma ya ce da zarar ya dawo zai karbi bakwancinta a ofisoshinsa da ke gidan gwamnati.

Martanin Hajara kan wannan kyauta

A cewarta:

"Da farko ina yi wa Allah godiya da ya ba ni wannan nasara saboda addu'ar da muke yi ne ta yi tasiri.
"Ina kuma mika godiya ga iyaye na da suka tsaya tsayin daka suka ba ni tarbiyya har na kai ga wannan nasara.

Hajara ta kara da cewa:

"Tabbas tsohon Ministan ya neme mu jiya har ya ba ni kyautar mota kuma ya ce har in kammala makaranta zai biya min.

Kara karanta wannan

"Akwai yunwa a kasar": Gwamnan PDP ya shiga zanga-zangar 'yan kwadago a jiharsa

"Na ji mai girma Gwamna ma ya ce idan ya dawo zai kirani, ina fatan Allah ya dawo da shi lafiya ya sanya alkairi a duk abin da zai faru."

Daliba ta lashe gasar musabaka ta duniya

Kun ji cewa wata daliba daga jihar Gombe ta yi nasarar lashe gasar musabaka ta duniya da aka yi a kasar Jordan.

Dalibar mai suna Hajara Ibrahim Dan'azumi daga unguwar Tudun Wada ta yi godiya ga Ubangiji kan wanna nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel