'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari Gidan Yari, Sun tafka Ɓarna

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari Gidan Yari, Sun tafka Ɓarna

  • Yan bindiga sun kai kazamin hari yankin gonar gidan gyaran hali a jihar Imo da sanyin safiyar ranar Litinin, sun tafka ɓarna
  • Maharan da ake kyautata zaton mayakan IPOB/ESN ne sun kashe ɗan sanda ɗaya kana suka yi awon gaba da jami'in gidan gyaran hali
  • Kwamishinan ƴan sanda ya lashi takobin farautar ƴan ta'addan waɗanda suka saki fursunoni bakwai yayin harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Wasu tsagerun ƴan bindiga sun halaka jami'in ɗan sanda ɗaya tare da kwance fursunoni bakwai yayin da suka kai hari gonar gidan gyaran halin Okigwe.

The Nation ta ruwaito cewa ƴan bindigan sun kai wannan hari yankin gidan gyaran halin da ke Okigwe a jihar Imo da sanyin safiyar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Ƴan kasuwa sun rage farashin kayan masarufi, talakawa zasu samu sauƙin sayen abinci

Yan bindiga sun kai hari a Imo.
Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro, sun kwance Fursunoni a gidan yarin Okigwe Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

An tattaro cewa maharan sun kuma yi awon gaba da jami’in hukumar gyaran hali da ke kula da yankin jim kadan kafin su kai hari gidan Sanata Patrick Ndubueze.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki rundunar ƴan sanda ta ɗauka?

Kwamishinan rundunar ƴan sandan jihar, Ɗanjuma Aboki, ya kai ziyara da kansa wurin da lamarin ya faru domin gane wa idonsa.

Yayin ziyarar, CP Ɗanjuma ya lashi takobin cewa rundunar ba zata huta ba har sai an kubutar da jami'in daga hannun ƴan ta'addan cikin ƙoshin lafiya.

Kwamishinan ya kuma ba da umarnin tura dakarun runduna ta musamman zuwa yankin domin su yi farautar maharan waɗanda ake kyautata zaton mayaƙan IPOB ne.

Su wa ake zargi da kai harin gidan gyaran hali?

A wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar Imo, Henry Okoye, ya fitar, ya zargi ƙungiyar ƴan aware IPOB da mayaƙanta ESN da kai wannan hari gidan gonar gidan yari a Okigwe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka ƴan kasuwa kusan 10 a jihar Arewa

Ya kuma rataya alhakin harin da aka kai gidan Sanata Patrick Ndubeze da safiyar ranar 12 ga watan Fabrairu a wuyan IPOB, rahoton The Cable.

"Harin ya yi sanadin sakin fursunoni bakwai da kuma sace jami'in hukumar gyaran hali guda ɗaya," in ji shi.

An kashe lauya a jihar APC

A wani ɓangaren, Rahotanni daga Kudu maso Gabashin Najeriya sun nuna cewa miyagun ƴan bindiga sun halaka lauya masanin doka, Victor Onwubiko, ɗan asalin jihar Imo.

Wata majiya ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Okigwe/Uturu tsakanin karfe 8 zuwa 9 na dare a ranar Asabar 10 ga watan Fabrairu, 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel