Sojoji Sun Kashe 'Yan IPOB/ESN, Sun Ceto Mutane 15 da Aka Yi Garkuwa da Su a Zamfara
- Sojojin Najeriya da ke aiki a Kudu maso Gabas sun kashe wasu mayakan Biyafra da kuma kungiyar tsaro ta Gabas (IPOB/ESN) guda biyar
- Hakazalika, takwarorinsu a Arewa maso Yamma, sun yi nasarar kubutar da mutane 15 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara
- A yayin hare-haren sojojin, sun kwato tarin muggan makamai tare da kakkabe 'yan bindigar yayin da wasu suka ranta a na kare zuwa daji
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Sojojin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun kashe wasu mayakan Biafra da kungiyar tsaro ta Kudu maso Gabas (IPOB/ESN) guda biyar.
An yi wannann musayar wutar ne a Ejemekuru da ke karamar hukumar Oguta ta jihar Imo, inda sojojin suka nuna wa tsagerun karfin damtse.
Sojoji sun kwato muggan makamai a Imo
Sojojin, wadanda suka hada da sojojin kasa da na ruwa, sun kuma gano “tarin muggan makamai” a farmakin da suka kai a ranar 1 ga Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Nation ta ruwaito cewa kakakin rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, 6 ga watan Maris.
A cewarsa, wasu daga cikin makaman da aka kwato sun hada da bindiga kirar AK-47, bindigogin 'Pump-action Semi-atomatik' biyu, da bindigar baushe daya.
...Sojoji sun ceto mutane 15 a Zamfara
The Cable ta ruwaito cewa, a wannan ranar ne, sojojin da ke yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso yammacin Najeriya sun ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su.
Nwachukwu ya ce an ceto mutanen ne a yankin Tsohuwar Tasha da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara, bayan kai wa al’ummar yankin dauki.
Ya ce:
“Dakarun sun kai daukin gaggawa inda suka yi artabu da masu garkuwa da mutane, azaba ta tilasta 'yan bindigar t tserewa tare da barin wadanda suka sace."
A cewar Nwachukwu, an kubutar da dukkanin mutanen 15 ba tare da dayansu ya samu wani rauni ba.
Sojoji sun kashe jagoran 'yan bindiga a Katsina
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar kashe Maikusa, babban jagoran 'yan bindiga da ke gudanar da ayyukan ta'addanci a jihar Katsina.
Manjo Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar ne ya sanar da hakan, inda ya ce sojoji sun yi artabu da 'yan bindigar a dazuzzukan kananan hukumomin Kurfi da Safana da ke jihar.
Asali: Legit.ng