'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta, Sun Kashe Mutum 7 Ƴan Gida 1 da Wasu Bayin Allah
- Wasu ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai mummunan hari a kauyen Azandeh a karamar hukumar Ukum ta jihar Benuwai
- Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kashe mutane da yawa cikin har ƴan uwan juna su 7, sun ƙona gidaje
- Shugaban karamar hukumar Ukum ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ya umurci a tura ƙarin jami'an ƴan sanda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Ƴan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe akalla mutum 10 a kauyen Azandeh da ke ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benuwai.
Amma mazauna kauyen sun bayyana cewa adadin waɗanda aka kashe a harin sun haura mutum 30, kamar yadda The Nation ta tattaro.
Daga cikin waɗanda maharan suka hallaka har da iyali mai ƙunshe da mutum 7 kuma mazauna sun faɗi sunayensu da Michael Mtindiga, Iorfa Michael Mtindiga, Akighirga, Tyowuese, Tersee Swende, Terngu Tortiv da Terkaa Shiati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga: Mahara suka ci karensu ba babbaka
Wani ganau, Tersoo Iorbee ya shaidawa ƴan jarida cewa sun samu labarin cewa wasu da ake zargin makiyaya ne na shirin kawo musu hari.
Iorbee ya ce:
"Bayan sama da sa'a ɗaya da samun wannan labarin, wasu ƴan bindiga da suka rufe fuskokinsu suka farmaki Azandeh, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
"Bayan ƙura ta lafa aka tabbatar da sun kashe mutum 10 ciki har da ƴan gida ɗaya su 7."
Haka nan kuma wani mazaunin ƙauyen, Msugh Aga, wanda ya tsira daga harin da kyar kuma ya yi gudun hijira zuwa wani gari ya ce:
"Makiyayan dauke da makamai sun buɗe wa jama'a wuta. Bayan haka, sai suka yi amfani da dogayen wuƙaƙe suka yanka su gunduwa-gunduwa. Sun kuma kona gidaje da dama.”
Wane mataki mahukunta suka ɗauka?
Kantoman karamar hukumar Ukum, Honorabul Victor Iorzaa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ya umarci DPO ya tura ƙarin jami'ai domin daƙile faruwar haka nan gaba, rahoton Naija News.
Ukum da ke kan iyaka da karamar hukumar Wukari a jihar Taraba na fama da yawan hare-hare daga wasu da ake zargin makiyaya ne.
Sojoji na ci gaban da samun nasara
A wani rahoton kuma Muhammad Badaru ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da samun galaba kan ƴan ta'adda a faɗin Najeriya.
Ministan tsaron ya ce a ƴan watannin da suka shuɗe, sojoji sun halaka manyan ƴan ta'adda akalla 7 a sassa daban-daban.
Asali: Legit.ng