Falgore: Kungiya Ta Nemi Alfarma Wajen Abba Yayin da Kwankwaso Ya Samu Mukami

Falgore: Kungiya Ta Nemi Alfarma Wajen Abba Yayin da Kwankwaso Ya Samu Mukami

  • An bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika dajin Falgore ga Gwamnatin Tarayya don tabbatar samun kulawa na musamman
  • Wata kungiya karkashin Friends of the Zoo, ita ta tura wannan bukata yayin bikin ranar Gandun Daji ta duniya a jihar Kano
  • Kungiyar ta bukaci hakan ne saboda Gwamnatin Tarayyar za ta fi bai wa dajin kulawa na musamman da ba shi kariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Wata kungiya karkashin Friends of the Zoo ta bukaci Gwamnatin jihar Kano ta mika dajin Falgore ga Gwamnatin Tarayya.

Kungiyar ta bukaci hakan ne saboda Gwamnatin Tarayyar za ta fi bai wa dajin kulawa na musamman da ba shi kariya.

Kara karanta wannan

Za a dauke wasu na'urori daga Kwalejin Zaria zuwa Legas? Gaskiya ta fito bayan zargin Dattawan Arewa

Abba Kabir zai mika wani muhimmin bangare na jihar Kano ga Gwamnatin Tarayya
An bukaci Abba Kabir ya mika dajin Falgore ga Gwamnatin Tarayya. Hoto: @KwankwasoRM.
Asali: Twitter

Wace bukata aka nema daga Abba Kabir?

Shugaba kungiyar, Abdullahi Baba Yahaya shi ya bayyana haka a Kano yayin ranar bikin Gandun Daji ta duniya, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, yayin bikin kungiyar ta bai wa tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso mukamin majibincin kungiyar.

Yahaya ya ce idan har ba a mika daji ga Gwamnatin Tarayya ba zai iya zama mafakar ‘yan bindiga da sauran masu laifuka.

Yayin da ya ke martani, Gwamna Abba Kabir wanda ya samu wakilcin kwamishinar Al’adu ya ce sun riga sun kafa kwamiti kan haka.

Martanin Abba Kabir kan wannan bukata

Kwamishinan, Ladidi Garko ta ce an kafa kwamitin ne karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin jihar, Dakta Abdullahi Bichi.

Garkot ace Abba Kabir ya himmatu wurin tabbatar da an mika dajin ga Gwamnatin Tarayya ba tare da wata matsala ba, Independent ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya tura a yi bikon Sheikh Aminu Daurawa ya dawo shugabancin Hisbah

Har ila yau, a jihar Kanon, Gwamna Abba Kabir ya shirya ba da kayan abinci ga mabukata yayin da ake shirin shiga watan Ramadan.

Gwamnan ya kafa kwamiti da za su yi aikin cikin tsari ba tare da samun wata matsala ba don taimakon jama’an jihar.

Gawuna ya ziyarci Kano

Kun ji cewa dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna ya samu kai ziyara jihar Kano a jiya Lahadi 3 ga watan Maris.

Gawuna ya samu tarbar dubban magoya bayansa wadanda suka taro shi daga filin jirgin saman Mallam Aminu Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel