Tsadar Rayuwa: Ministan Tinubu Ya Fadi Dalili 1 da Ya Sa Mutanen Yankinsa Ba Za Su Yi Zanga-Zanga Ba
- An yi kira ga ƴan Najeriya da su nuna kishin ƙasa maimakon yin zanga-zanga a cikin wannan mawuyacin hali na tattalin arziƙi
- Ministan ayyuka, Dave Umahi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a garin Uburu na jihar Ebonyi
- Tsohon gwamnan na jihar Ebonyi ya kuma bayyana dalilin da ya sa yankin Kudu maso Gabas zai ci gaba da ƙauracewa zanga-zangar adawa da Shugaba Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Uburu, jihar Ebonyi - Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa mazauna yankin Kudu maso Gabas ba za su shiga zanga-zangar nuna adawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba kan tsadar rayuwa.
Umahi ya jaddada cewa Tinubu ya yi maganin rikicin manoma da makiyaya da ke da haifar da rashin tsaro da ƙarancin abinci a yankin.
Minista ya yi magana a kan tsadar rayuwa
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, ministan, yayin da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa ta Uburu, jihar Ebonyi, ya yi magana kan matsalar tsadar rayuwa a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umahi ya alaƙanta hakan kan sakaci da gwamnatocin baya suka yi, wanda Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin magancewa ta hanyar manufofi da tsare-tsare masu kyau.
Ya yi nuni da cewa yankin Kudu maso Gabas ya samu tagomashi a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, ciki har da naɗe-naɗen muƙamai kamar nasa a matsayin ministan ayyuka na farko daga yankin, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Umahi ya buƙaci ƴan Najeriya su kasance masu kishin ƙasa
Ministan ya ce mutanen yankin Kudu maso Gabas ba su da wata hujjar yin zanga-zanga da nuna adawa da Shugaba Tinubu kan tsadar rayuwa.
Umahi ya shawarci jama’ar yankin da kada su shiga zanga-zangar da ake yi domin nuna adawa da Shugaba Tinubu.
Da yake sukar zanga-zangar da ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta jagoranta a baya bayan nan, tsohon gwamnan na jihar Ebonyi ya yi nuni da cewa ba ta dace ba.
Ya yi kira ga ƴan Najeriya da su baiwa kishin ƙasa fifiko, kuma su guji yin ayyukan da za su kawo cikas ga ci gaban ƙasar nan.
NLC Ta Dakatar da Zanga-Zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta dakatar.da.zanga-zangar da ta fara a faɗin ƙasar nan kan tsadar rayuwa.
Ƙungiyar ta dakatar da zanga-zangar ne bayan ta bayyana cewa ta cimma maƙasudin zanga-zangar da ta gudanar.
Asali: Legit.ng