'Dan Gida Ya Fasa Kwai, Ya Jefi Gwamnatin Tinubu da Biyewa Manufofin Turawa
- Tsohon mataimaki shugaban APC na shiyyar Arewa bai jin dadin kamun ludayin gwamnati mai-ci
- Salihu Mohammed Lukman ya soki salon mulkin Bola Ahmed Tinubu duk da suna tare a jam’iyyar APC
- ‘Dan siyasar yana ganin cewa Tinubu da Buhari ba su da wani buri illa su hau kujerar mulki a Najeriya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Salihu Mohammed Lukman wanda ya taba zama cikin wadanda ake rufe kofa da su a jam’iyyar APC ya soki gwamnati mai-ci.
Salihu Mohammed Lukman ya zargi Bola Ahmed Tinubu da tafiyar da gwamnatin tarayya tamkar a mulkin soja, ya ce bai yi da kowa.
Lukman ya sake caccakar APC
Tsohon mataimakin shugaban na APC ya zargi shugaban Najeriya da yi tamkar ya san duk mafitar matsalolin da suka addabi kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a shawo kan matsalolin zamantakewa da tattalin arzikin da ake fuskanta ba, Lukman yana ganin akwai barazana a zaben 2027.
Tinubu ya dauko manufofin IMF
Jagoran na jam’iyya mai ci ya fitar da jawabi na musamman a ranar Asabar, ya koka game da talauci, yunwa da kuncin da aka jefa jama'a.
‘Dan siyasar yana ganin tsare-tsare da manufofin IMF aka dauko ganin yadda aka cire tallafin man fetur kuma aka karya kimar Naira.
Lukman wanda ya rubuta littafi kwanaki a game da shugabanci, yana ganin Bola Tinubu ya kama hanyar da Muhammadu Buhari ya bi.
Daily Trust ta rahoto shi yana cewa ba alkawarin da aka yi wa mutanen Najeriya kenan ba, yana mamakin yadda Tinubu zai zarce a ofis.
Jawabin Salihu Luqman a kan Tinubu
"Idan yana so ya zarce, meyasa yake tafiyar da gwamnati kamar soja, yana toshe shugabannin jam’iyya kuma yana raina al’umma kamar wani sarkin da yake da ilmin duk abin da zai sa al’umma farin ciki
Sai dai idan ana so a zarce ne ba ta hanyar samun kuri’un mutane ba, amma babu wani dalili."
- Salihu Mohammed Lukman
'Dan APC ya soki Tinubu, Buhari
A jawabinsa, Lukman ya ce wasu ‘yan APC da aka fusata suna tunanin Muhammadu Buhari da Tinubu mulki kurum suke so ba komai ba.
Bayan sun cin ma burinsu, sai aka yi wasti da duk wasu tsare-tsaren da za su taimaki jama’a, an biye shawarwarin masanan yamma.
Buhari ya yi wa gwamnatin Tinubu bayani
Ana da labari Muhammadu Buhari ya fadawa gwamnatin Bola Tinubu abin da ya faru da aikin wutar Mambilla a wata takarda da ya aika.
Buhari ya sanar da Lateef Fagbemi SAN cewa bai ba ministocinsa umarnin a biya wasu kudi ko a sasanta da kamfanin Sunrise Power ba.
Asali: Legit.ng