‘Yan Daudu Sun Farmaki Ofishin Hisbah a Kano Tare da Yin Fashe-Fashe, An Gano Dalili

‘Yan Daudu Sun Farmaki Ofishin Hisbah a Kano Tare da Yin Fashe-Fashe, An Gano Dalili

  • 'Yan daudu sun taru sun kai hari ofishin hukumar Hisbah da ke unguwar Bachirawa karshen kwalta a jihar Kano
  • Tsagerun sun farfasa motar 'yan Hisbar tare da basu umurnin sako 'yan uwansu da ke tsare a hannunsu hukumar
  • Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban hukumar da ke yaki da badala a jihar, Sheikh Aminu Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Kano - Yayinda da ake 'yar tsama tsakanin hukumar Hisbah da gwamnatin Kano, wasu da ake zaton 'yan daudu ne sun farmaki ofishin hukumar da ke Bachirawan a jihar.

Al'ummar unguwar Bachirawa karshen kwalta sun nuna damuwarsu kan harin da 'yan daudun suka kai ofishin 'yan Hisbah a yankinsu.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun farmaki manoma a Borno, sun halaka mutum 3 da sace kekuna 50

'Yan daudu sun farmaki ofishin Hisbah
‘Yan Daudu Sun Farmaki Ofishin Hisbah a Kano, Sun Yi Fashe-Fashe Hoto: Getty Images
Asali: Facebook

Me yasa 'yan daudu suka farmaki ofishin Hisbah?

Dala FM ta rahoto cewa tun da farko wata kungiya da ke kare unguwar ta ga wasu matasa da take zargin 'yan kungiyar asiri ne da misalin karfe 3:00 na dare, suna zagaye gidan turuwa tare da gabatar da bukatunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan sai mutanen suka watsa nono, gero da turare da sauran abubuwa a gidan tururuwar kamar dai masu tsafi.

A cewar shugaban kungiyar kare unguwar ta Bachirawa, Abubakar Alhassan Datti, bayan an kora matasan sai suka shiga gidan wani 'dan daudu.

Datti ya ce bayan nan sai aka mika kayayyakin da mutanen suka zuba a ramin tururuwan ga ofishin Hisbah, inda su kuma 'yan daudun suka far masu har da farfasa motar 'yan Hisbar, rahoton Leadership.

'Yan daudu sun nemi Hisbah ta sako mutanensu

Kara karanta wannan

An tarwatsa masu zanga-zanga kan harin 'yan bindiga a jihar Arewa

An kuma rahoto cewa 'yan daudun sun yi danzadazo dauke da muggan makamai, inda suka farmaki ofishin Hisbar na unguwar Bachirawa bayan sun nemi a sako mutanensu biyu da aka kama.

Sun kuma nemi a dawo masu da kayan tsafinsu da al'ummar unguwar suka mikawa 'yan Hisbar.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban hukumar Hisbah a jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa.

Daurawa ya hakura da kujerarsa ne bayan gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya fito ya soki ayyukansu a bainar jama'a, lamarin da ya tayar da kura a tsakanin al'umma.

Duk wani kokari da jaridar Legit ta yi don jin ta bakin kan wannan lamari ya ci tura, domin dai lambar wayarta baya zuwa.

Jigon APC ya magantu kan rikicin Abba da Daurawa

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ismaeel Buba Ahmed, ya yi martani akan sabanin da ya shiga tsakanin hukumar Hisbah ta Kano da gwamnatin jihar.

Alaka dai ta yi tsami tsakanin gwamnatin Abba Kabir Yusuf da hukumar Hisbah a jihar Kano, inda har gwamnan ya fito ya soki ayyukan hukumar a bainar jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel