Daurawa v Abba: Malamai da Manya Sun Yi Maganganu Kan Murabus Din Shugaban Hisbah

Daurawa v Abba: Malamai da Manya Sun Yi Maganganu Kan Murabus Din Shugaban Hisbah

  • Tun a jiya aka ji Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya yi magana game da ajiye aikin Aminu Ibrahim Daurawa
  • Shugaban Izala yana ya roki gwamnan da aka fi sain da Abba Gida Gida ya yi hakuri ya cigaba da aiki da malamin
  • Malam Ahmad Muhammad Gombe ya ce kowa da irin yadda yake kallon murabus din da malamin ya yi daga Hisbah

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Tun da labari ya zagaya cewa Aminu Ibrahim Daurawa ya bar shugabancin Hisbah a jihar Kano, jama’a suka shiga fara yin maganganu.

Rahoton nan ya tattaro kalaman da aka ji daga bakin shugabanni da jagororin al’umma a kan sabanin da aka samu da shugaban a Hisbah.

Kara karanta wannan

"Allah ya sa malam ya hakura": Jigon APC ya magantu kan sabanin Daurawa da gwamnatin Kano

Kano Daurawa
Sheikh Aminu Daurawa ya bar Hisbah a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf da Aminu Daurawa
Asali: Facebook

Rijiyar Lemo ya yabi aikin Daurawa da Hisbah

Tun a ranar Juma’a, Legit ta samu labari babban malami, Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo ya koka game da yadda ake neman lalata jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban malamin ya ce garin Kano da ya yi fice da yaki da munanan halaye, yana neman zama hedikwatar badala a Arewacin Najeriya.

Sani Umar Rijiyar Lemo ya ce bata-gari suna baro garuruwansu zuwa Kano inda suke cin karo da ‘yan Hisbah da Aminu Ibrahim Daurawa.

Hisbah: Gadon Kaya yana so a bar Sheikh Daurawa

Aminiya ta ce shi kuwa Dr. Abdullahi Umar Gadon Kaya ya yabi alheran da gwamnatin Mai girma Abba Kabir Yusuf ta zo da shi.

A hudubar da ya gabatar jiya, Abdullahi Umar Gadon Kaya ya nemi gwamna ya tattauna da Aminu Daurawa domin warware sabaninsu.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso ya yi martani kan murabus din Daurawa daga shugabancin Hisbah, ya yi gargadi

Malamin yana so a ba Sheikh Daurawa hakuri, ya koma jagorantar rundunar Hisbah a jihar. Wannan shi ne ra'ayin har wasu 'yan siyasa.

Nasihar Sani Yahaya Jingir ga Abba, Daurawa

Dattijo kuma jagoran kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi nasiha ga gwamnan Kano ya yi hakuri ya yi aiki da Aminu Daurawa.

A wani bidiyo, Sani Yahaya Jingir ya kira tsohon shugaban na Hisbah da kaninsa, ya ce bai dace shaidan ya shiga tsakaninsa da Abba Yusuf ba.

Malamai irinsu Ahmad Muhammad Gombe sun tofa albarkacin bakinsu a hudubar Juma’a, yake cewa mutane sun rabu kan abin da ya faru.

Sheikh Ahmad Gombe ya ce tun farko akwai wadanda ba su son ganin alherin gwamnatin NNPP.

Kano: Madakin Zazzau bai ji dadi ba

Madakin Zazzau, Munir Jafaru a wajen bude wani masallaci a garin Kano ya yi magana bayan jin Aminu Daurawa ya ajiye aikinsa Kano.

Kara karanta wannan

Hisbah Kano: Tsohon hadimin Buhari ya magantu kan murabus ɗin Sheikh Daurawa

Alhaji Munir Jafaru ya nuna gwamnatin Kano ta ba ta kyautawa malamin musuluncin ba.

Yadda Abba ya fusata Daurawa

Daga dawowa daga Saudiyya, rahoto ya zo maku cewa Abba Kabir Yusuf ya yamutsa jihar Kano wajen sukar aikin Hisbah a karkashinsa.

Abba ya fadawa Hisbah ko da gyara za ayi dole ne bin doka da bin tsari, tun nan aka san akwai matsala tsakaninsa da malamin musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel