Bayan Shekaru da Dama, Magidanci Ya Gano Ba Shine Mahaifin ‘Diyarsa Mai Shekaru 18 Ba
- Wani mutumi ya shiga rudani bayan ya gano yaudarar da aka yi masa tsawon shekaru 17 game da ainahin uban 'diyarsa
- Ya gano gaskiya game da wanda ya haifi 'diyar tasa mai shekaru 18 ne a lokacin da ya yi niyar dawo da ita kasar Amurka
- Makwabcin mutumin a Amurka ya yi karin haske kan abin da ya aikata bayan gano hakan, lamarin da ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Zuciyar wani 'dan kasar Jamaica ta karaya bayan ya gano cewa ba shi ne uban 'diyarsa, wacce ta shekara 18 ba.
Innocent Tino, wani mai watsa shirye-shirye a Facebook mazaunin birnin New York, shine ya ba da labarin mai karya zuciya a dandalin soshiyal midiya kuma ya haddasa cece-kuce.
A cewar Innocent, gidan mutumin na kusa da nasa kuma ya rufe kansa a gida tsawon kwanaki uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin 'dan kasar Jamaica ya yi nufin kawo 'diyarsa US lokacin da ya gano cewa ba tasa bace. Innocent ya rubuta:
"Watau wani 'dan Jamaica da ke zama kusa da ni ya ki ganin kowa kwanaki 3 kenan ya kulle kansa a cikin gida saboda ya so kawo 'diyarsa mai shekaru 18 Amurka daga Jamaica lokacin da ya bayyana cewa ba shi ne ubanta ba. Mutumin ya karaya."
Wani rahoto daga cibiyar gwajin DNA ya bayyana cewa kaso 26 cikin 100 na mazan Najeriya ba sune iyayen yaransu ba.
Jama'a sun yi martani
Ellen Nnenna Chidi-Ezeama:
"Oh, amma hakan abun bakin ciki, damuwa da rashin adalci ne!!"
Chichi Chukwunonye ya ce:
"Ku kwantar da hankalinku..na'urar bature na yin kuskure."
Lenin Park ya ce:
"Sanarwa!!
"Mutumin da ya ce, wanda ya samu mace ya samu farin ciki....Ya ba da hakuri."
Kakakin 'yan sandan Gombe ya angwance
A wani labarin kuma, kakakin 'yan sandan jihar Gombe, Mahid Abubakar, ya angwance da kyakkyawar amaryarsa mai suna Nafisa a ranar Asabar, 24 ga watan Fabrairu.
Sai dai kuma, labarin soyayyarsu da jami'in 'dan sandan ya bayar a shafinsa na X a ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, shine babban abin da ya dauki hankalin jama'a.
Asali: Legit.ng