Wani Mutum Ya Hadu Da Bugun Zuciya Bayan Gano Yayan Da Yake Daukar Dawainiya Ba Nasa Bane

Wani Mutum Ya Hadu Da Bugun Zuciya Bayan Gano Yayan Da Yake Daukar Dawainiya Ba Nasa Bane

  • Wani dan Najeriya ya yanke jiki ya fadi bayan samun mumunan labari, jikin ya shanye kwata-kwata
  • Mutumin ya kama matarsa ne da wani kwarto yana yi masa zagon kasa wanda hakan ya janyo fada tsakaninsu
  • A yayin fadan ne matar ta bayyana cewa ‘ya’yansu biyu ba nasa ba ne, wanda hakan ya sa ya fadi

Duniyar wani dan Najeriya ta shiga tsaka mai wuya bayan da matarsa ​​ta bayyana masa cewa ‘ya’yansu biyu ba nasa ba ne.

A cewar @MaverickThamani wanda ya bayyana wannan lamari mai ban tausayi a shafin Twitter, mutumin da ke da shekaru kusan 50 sai da aka kwasheshi bayan sanar da shi labarin.

Mutumin yana girmama matarsa da jin maganarta fiye da yadda yan uwansa ko abokansa suke fada masa, wato abinda hausawa suke cewa "mijin tace".

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Tsinke Mijinta Da Mari Ana Tsaka Da Bikin Aurensu, Shima Ya Rama

Rayuwa
Ko Da Sandar Dogarawa Wajen Tafiya, Baya Iya Yi: Mutumin Da Ya Samu Bugun Zuciya Ya Fadi Hoto: Getty
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanar da shi din yazo ne lokacin da suke fada da matar wanda cece-cece kucen a tsakaninsu ta janyo ta fada masa maganar.

“Dan ta bakantawa mutumin sabida da fadan da suke sai ta fasa kwai.
"Wai kai namiji ne ma? Shin za ka iya yiwa mace ciki? To yaran nan ba naka ba ne."
“Mutanen da suka zo raba fada duk sun yi kokarin tsawatar mata da tunanin fushi ne. Amma ina?

.....kamar yadda Thamani ya rubuta

Nan take mutumin ya fadi ya hadu da bugun zuciya. Matar kuwa tai masa kan kaf a susun bankinsa tare da tafiya da yaran.

“Kafin kace me yara sun girgije da kudin shi kuma mutumin jininsa ya hau.

Kara karanta wannan

Ta bare: Saura kiris biki ango ya gano budurwarsa na da 'ya'ya 2, ya dauki tsattsauran mataki

"Sun ce ya riga ya bugun zuciya." (kamata yai a nesantashi da matar)

Matar mai suna Queen Jezebel ta yashe asusun ajiyarsa sabida dama tana da masaniya kan bayanansa kuma ta tafi da 'ya'yan

Ra'ayoyin Masu Amfani da Kaafafen Sadarwa

@ibrokolawole ya ce:

"Idan wannan bai zama me maka darasi ba, ba abinda zai zame maka to, wannan shi ke nuna kar ka yanke alaqa da yan uwanka na jini sabida mace ko kuma sabida wani abun mai kama da haka, wannan izina ne ga kowa kan matan zamani."

@SoloJah1 ya ce:

"Gaskiya na jiye mutumin nan ciwo haba wa abin ba dadi, shi yasa ake cewa naka-naka ne, kmar yadda wani aktan fin yake fada karka juyawa ahlinka baya."

@MaxwellBobo1 ya ce:

"Abinda ba ka sani ba shine kae ka nuna kudin wajen aure"

@oluchukwunzewi Yace:

"Yawancin lokuta za su ce ka sami kudi kafin ka auri , ka zo ka sami kudi ka auro wahala , kai da matarka amma ta janyo ma bala'i."

Kara karanta wannan

"Ku Wuce Ɗaki": Wani Mutumi Ya Sunkuci Matarsa Yayin da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Bidiyon Ya Ja Hankali

@martinosofr ya ce:

“Kafin in yi aure, zan kira ahlina,in ce in sun ga matata zata kaini ga halaka to su raba auren.

Wani mutum ya gano bayan gwajin DNA na sirri cewa 'yarsa ba tasa ba ce

A wani labarin mai kama da wannan, Legit.ng ta rawaito a baya cewa wani mutum ya gano cewa diyar sa ba ta sa ba ce bayan ya yi gwajin kwayoyin halitta DNA.

A cikin wani faifan bidiyo na TikTok wanda ya yadu, mutumin nunawa matarsa sakamakon gwajin DNA a madafar abinci.

Tayi kokarin bude sakon a cikin takardar sako mai launin ruwan kasa da zumudi tana tunanin ko tikitin hutu ne.

Daga nan sai fada mata cewa sakamakon gwajin DNA da ya gudanar a asirce ne ya nuna ‘yarsa ba shi ya haifeta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags:
Online view pixel