Cin amana tsagoransa: Wata mata ta shaidawa mijinta cewa ba shine uban 'yayansu 3 ba

Cin amana tsagoransa: Wata mata ta shaidawa mijinta cewa ba shine uban 'yayansu 3 ba

- Wata mata, Mayowa ta shigar da mijinta kara a kotun al'adu da ke Ibadan kan cewar mijin baya kula da ita da yaranta guda 3

- Mayowa ta kuma shaidawa kotun cewar mijinta ya dauki dabi'ar sa ido akan dukkanin wayoyin da take yi da kawayenta da kwastomominta, wanda sam ba zata lamunci hakan ba

- Sai dai mijin, Aderibigbe Adedolapo, ya ce matarsa ta tabbatar masa cewa 'yayansu guda 3 ba shine ubansu ba, duk da irin namijin kokarin da yake yi na ganin ya kyautata masu

A ranar litinin, 24 ga watan Disamba 2018 ne wani magidanci Aderibigbe Adedolapo, zai tabbatar da makomarsa a wata kotun al'adu ta Oja-Oba da ke garin Mapo, Ibadan, kan wata kara da matarsa, Mayowa, ta shigar dangane da aurensu na shekaru 8.

Mayowa ta bukaci kotun da ta raba aurenta da Adedolapo, tana mai ikirarin cewa baya kula da ita da yaranta da kuma tsananin binciken da yake yi a wayarta, wanda hakan alamar zargice.

Wacce ta shigar da karar, mai zama a Apete, Ibadan, ta sanar da kotun cewa mijinta ya dauki dabi'ar sa ido akan dukkanin wayoyin da take yi da kawayenta da kwastomominta, wanda sam ba zata lamunci hakan ba.

Ta ce akwai lokacin da Adedolapo ya taba yin barazanar kasheta da fasassar kwalba.

KARANTA WANNAN: 2019: Wata kungiya tayi zargin cewa akwai jigogin APC da ke adawa da tazarcen Buhari

Cin amana tsagoransa: Wata mata ta shaidawa mijinta cewa ba shine uban 'yayansu 3 ba
Cin amana tsagoransa: Wata mata ta shaidawa mijinta cewa ba shine uban 'yayansu 3 ba
Asali: Depositphotos

Mayowa ta kuma buga misali da wani al'amari da ya faru a baya, inda mijinta ya duketa, ya yi mata tsirara tare da fito da ita daga cikin kewaye, wanda ya kunyatar da ita a gaban makwabtansu.

Sai dai a bangaren Adedolapo, ya tabbatar da cewa suna samun sabani da yin fada lokaci zuwa lokaci, inda ya bayyana matarsa a matsayin mai son rikici wacce take ganin zata iya dukan kowa, komai shekarun mutum.

Ya ce babban abunda ke ci masa tuwo a kwarya baya wuce yadda matarsa ta tabbatar masa cewa 'yayansu guda 3 ba shine ubansu ba, duk da irin namijin kokarin da yake yi na ganin ya kyautata masu.

Adedolapo ya yi nuni da cewa matarsa takan yi tafiya wajen birnin Ibadan ba tare da saninsa ba, wasu lokutan ma takan kauracewa gidan gaba daya na tsawon lokaci.

A yayin jin ra'ayoyinsu gaba daya, Mayowa ta karyata zargin mijin na cewar tana mu'amala da wasu mazan a waje. Sai dai ta ce tunda har mijin yana zarginta kan yaransu ba nashi bane, to ita zata nema masu wani uban.

Mai shari'a a kotun, Chief Odunade Ademola, ya umurcin Mayowa ta gabatarwa kotun yaran nasu guda 3 a zaman da zata yi ranar 24 ga watan Disamba, 2018 don ci gaba da sauraron karar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel