Mijina ya san ba shine uban yara hudu da na haifa ba saboda ya san ba ya haihuwa - Bazawara

Mijina ya san ba shine uban yara hudu da na haifa ba saboda ya san ba ya haihuwa - Bazawara

Wata mata mai suna Maria Mthembo, 'yar asalin kasar Zimbabwe, ta fito fili ta fadi gaskiya, inda ta bayyana yadda ta kwashe tsawon shekaru 10 tana cin amanar mijinta da makwabcinsu, lamarin da ya kai har sun haifi yara hudu.

A cewar wata jaridar kasar Zimbabwe mai suna iHarare, Maria ta fadi gaskiyar ne bayan an kama ta dumu-dumu tare da makwabcinsu mai suna Amos Paradzai suna lalata.

Rahotanni sun bayyana cewa Maria tare da mijinta Erick Moyo na zaune a kauyen Ndandulo da ke Gokwe. Erick, mijin Maria, ya mutu kimanin watanni biyu da suka gabata.

Surukan Maria sun zarge ta da mayar da gidan dan uwansu da ta aura wurin bariki da sheke aya bayan mutuwarsa.

DUBA WANNAN: Amarya ta fadi sumammiya ranar biki bayan ta gano wani boyayyen sirri a kan angonta

Wata majiya ta shaida wa iHarare cewa, "surukanta basu ji dadin rayuwar da ta fara ba bayan watanni biyu kacal da mutuwar mijinta, sun nuna fushinsu a kan rashin daraja dan uwansu ta hanyar mayar da gidansa wurin hole wa.

"Da suka yi mata tistiye ne ta tabbatar musu da cewa ba tsohon mijinta ne uban yara hudu da suka haifa ba, tare da fada musu cewa Paradzwa ne uban yaran."

Da aka gurfanar da ita a gaban wata kotun gargajiya, Maria ta shaida wa mai shari'a cewa mijinta ba ya haihuwa kuma ya san cewa ba shine uban yaran da ta haifa ba, duk da bai san waye ubansa na gaskiya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel