Tsadar Rayuwa: Fursunoni Sun Fusata, Sun Yi Zanga-Zanga a Jihar Arewa

Tsadar Rayuwa: Fursunoni Sun Fusata, Sun Yi Zanga-Zanga a Jihar Arewa

  • Fursunonin gidan gyara hali na Jos sun gudanar da zanga-zanga a ranar Juma'a, 1 ga watan Maris, kan yunkurin rage yawan abincinsu
  • Fursunonin sun nuna rashin gamsuwa da wannan matakin, lamarin da ya tursasa hukumar gidan yarin harba barkonon tsohuwa don daidaita lamarin
  • Shugaban gidan gyara hali, Raphael Ibinuhi, ya tabbatar da zanga-zangar, inda ya danganta lamarin da tsadar kayan abinci a kasuwa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Plateau - Zanga-zangar da ake yi a fadin kasar saboda tsadar kaya ta kai gidan gyara hali na Jos, babban birnin jihar Filato.

A ranar Juma’a, 1 ga watan Maris ne fursunoni suka gudanar da zanga-zanga kan shirin rage yawan abincin da ake basu.

Fursunoni sun yi zanga-zanga a Jos
Tsadar Rayuwa: Fursunoni Sun Fusata, Sun Yi Zanga-Zanga a Jihar Arewa Hoto: DoxaDigtial, Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Yadda fursunoni suka yi zanga-zanga

Kara karanta wannan

An tarwatsa masu zanga-zanga kan harin 'yan bindiga a jihar Arewa

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa fursunonin sun fara zanga-zanga ne jim kadan bayan sun samu labarin zabtare yawan abincin da ake basu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin zanga-zangar, fursunonin sun ki bin umurnin da jami’an gidan yarin suka basu sannan suka kuma kauracewa abincin safe.

Sun taru ne a tsakiyar farfajiyar gidan yarin yayin da suke ta daga muryoyinsu don nuna turjiya.

Sai dai kuma jami’an tsaron gidan yarin sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen mayar da su dakunansu.

Me hukumar gidan yari ta ce kan zanga-zangar?

Shugaban gidan gyara hali na Jos, Raphael Ibinuhi, ya tabbatar da zanga-zangar da fursunonin suka yi, rahoton Trust Radio.

Ibinuhi ya ce:

“Matsalar na da nasaba da tsadar kaya a kasuwa. ‘Dan kwangilar da ke kula da abincin ya ce farashin kayan abinci ya tilasta musu rage yawan abincin.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata, sun fito zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga a jihar Arewa

“Don haka, adadin abincin ne ya haifar da zanga-zangar. Bana tunanin zanga-zangar na da amfani saboda matsalar abinci da tsadar kaya abu ne na kasa da gwamnatin tarayya ke aiki a kai.
“Kuma ina ganin tun da abu ne na kasa, duk matakin da gwamnatin tarayya ta dauka don magance shi za a ji shi a ko’ina a kasar ciki harda gidajen gyara hali.”

Tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar na ci gaba da haifar da zanga-zanga a yankuna daban-daban na kasar.

A ranar Litinin ne kungiyar kwadago ta kasa ta tara mambobinta a fadin kasar domin yin zanga-zanga, lamarin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana a matsayin ba abin yarda ba.

Gwamnati za ta bayar da tallafi

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin Najeriya ta bayyana abubuwan da ake buƙata domin shirin bayar da tallafin kuɗaɗe ga iyalai miliyan 15 da ke fama da matsalolin tattalin arziƙi.

Shugaba Bola Tinubu ya ji koke-koken ƴan Najeriya game da hauhawar farashin kayayyakin abinci, ya kuma tabbatar da aniyar dawo da tallafin kuɗaɗe ga mabuƙata da iyalai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng