Dangi Sun Shiga Makoki Yayin da Tuwo Ya Kashe Mutum, Aka Kwantar da 4 a Asibiti
- Wata karamar yarinya ta mutu yayin da aka kwantar da mutum hudu a asibitin koyarwa na LAUTECH, jihar Oyo bayan cin tuwon alabo
- Jim kadan bayan kammala cin abincin ne suka fara korafin ciwon ciki, wanda ya zama silar ajalin yarinyar wadda jika ce a gidan
- Rahotanni sun bayyana cewa iyalan sun yi amfani da bawon rogo wanda suka nika tare da mayar da shi tuwon alabo, saboda talauci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Oyo - A yayin da ‘yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa a kasar, an garzaya da mutum shida 'yan gida daya bayan da suka ci tuwon alabo zuwa asibitin Ladoke Akintola.
Lamarin da ya faru a karamar hukumar Ogbomoso ta Kudu/Ogo Oluwa a jihar Oyo wanda ya yi sanadin mutuwar daya daga cikin mutanen.
Vanguard ta tattaro cewa wani kiran gaggawa da aka yi ya ja hankalin makwabtan wadanda abin ya shafa a yankin Temidire Atoyebi da ke Ogbomoso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma tattaro cewa wannan mummunan lamari da ya afku a ranar Laraba ya faru ne bayan da iyalan suka ci tuwon da daddare.
Jikar gidan ta mutu kafin zuwa asibiti
Jim kadan bayan kammala cin tuwon ne suka fara korafin ciwon ciki, wanda ya zama silar ajalin yarinya daya wadda jika ce a gidan.
Makwabta sun garzaya da iyalan Misis Victoria Adewole da yara hudu zuwa asibitin Ogo Oluwa, daura da babbar makarantar Ogbomoso.
Bayan isowarta asibitin ne aka tabbatar da mutuwar yarinyar tare da kwantar da sauran mutum hudu a bangaren bada kulawa ta musamman.
Talauci ne ya jefa iyalin a halin da suke yanzu
Jaridar The Nation ta gano cewa iyalan sun yi amfani da bawon rogo wanda suka nika tare da mayar da shi tuwon alabo, kasancewar ba su da kudin sayen doya ko garin rogon.
“Mahaifiyar da sauran ‘ya’yanta hudu har yanzu suna kwance a asibiti, rai hannun Allah. Muna rokon jama'a su taimaka wa iyalin ta duk hanyar da za su iya."
- A cewar wata majiya.
Babban daraktan asibitin koyarwa na LAUTECH, Farfesa Olawale Olakulehin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Uwa da ƴaƴanta da karen gidansu sun mutu bayan cin Amala
Ba wannan ne karon farko da irin hakan ta faru ba, a baya ma Legit Hausa ta ruwaito yadda wata uwa da ƴaƴanta suka ci tuwon amala suka mutu a jihar Ekiti.
Yayin da mijin ya ke kwance a asibiti rai hannun Allah, su ma karnuka biyu na gidan da suka ci tuwon sun bakunci lahira.
Wannan lamari ya daga hankulan jama'ar yankin Ikole, tare da jefa su cikin juyayi na mutuwar farat ɗaya da iyalin gidan suka yi.
Asali: Legit.ng