Wata uwa da 'ya'yanta da karen gidansu sun mutu bayan sun ci tuwon Amala

Wata uwa da 'ya'yanta da karen gidansu sun mutu bayan sun ci tuwon Amala

Al'umar garin Odo-Ayedun da ke yankin Ikole a jihar Ekiti sun tsinci kansu cikin halin juyayi, sakamakon mutuwar wata uwa da 'ya'yanta bayan sun ci tuwon amala, wacce ake sarrafa wa daga fulawar garin rogo.

Mijin matar, mai shekaru fiye da 50, yana kwance cikin mawuyacin hali a asibitin koyar wa a Ido Ekiti, inda likitoci ke kokarin kwato ran shi saboda cin tuwon amalar.

Wasu karnuka guda biyu da aka tabbatar sun ci tuwon amalar, su ma sun mutu.

Daya daga cikin 'ya'yan matar yana da shekaru 12, shi kuma dayan shekaru 14.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Ekiti, Caleb Ikechukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Ya ce rundunar 'yan sanda zata hada hannu da sauran hukumomi domin binciko sababin mutuwar mutanen.

Adeoye Aribasoye, mamba mai wakiltar mazabar Ikole a majalisar dokokin jihar Ekiti, ya bukaci a gaggauta gudanar da bincike a kan lamarin yayin da ya gabatar da batun a zauren majalisar dokokin ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: Zan fada rijiya idan ba a raba aurena da ita ba - Miji ya nemi kotu kotu ta raba aurens da matarsa bayan shekaru 40

Ya ce marigayiyar ce ta sarrafa tuwon Amalar kuma ta raba ta bawa kowa a matsayin abincin dare.

Kazalika, Mista Aribasoye ya koka a kan halin ni 'yasu da asibitin garin Odo Ayedun ke ciki, lamarin da ya ce ya jawo asibitin ya gaza bayar da agajin gaggawa domin ceto rayuwar mutanen da iftila'in ya fada wa.

Da yake martani a kan faruwa lamarin, shugaban majalisar dokokin jihar Ekiti, Funminiyi Afuye, ya mika sakon ta'aziyya ga dangin mamatan da kuma jama'ar mazabar Ikole a kan faruwar lamarin.

Shugaban majalisar ya umarci kwamitin harkokin lafiya da ya fara gudanar da bincike a kan abin da ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng