Yadda a garin cin Tuwon Amala, mutane 2 suka riga mu gidan gaskiya

Yadda a garin cin Tuwon Amala, mutane 2 suka riga mu gidan gaskiya

Mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya a garin Obokun dake jihar Osun, yayin da aka samu wasu su hudu da shiga mawuyacin hali bayan sun ci tuwon Amala da miya a ranar juma’a 27 ga watan Oktoba.

Mutanen sun mutu ne bayan sun kammala cin Tuwon, daya daga cikinsu Uwargida Kehinde Fasanya, ma’aiakciya ce a karamar hukumar Obokun, sai dai ba’a bayyana sunan dayan mamacin ba.

KU KARANTA: Matasa su yi koyi da Dattijon arziki, na tabbatar da gaskiyar sa – Buhari ga Balarabe Musa

Tuni aka garzaya da gawan su zuwa babban asibitin jihar Osun dake garin Osogbo don tabbatar da gaskiyar lamarin, yayin da aka garzaya da sauran mutane hudu zuwa wani Asibitin don samun ingantaccen kulawa.

Yadda a garin cin Tuwon Amala, mutane 2 suka riga mu gidan gaskiya
Motar data dauki gawansu

Daily Trust ta ruwaito mutuwar mutanen ya janyo jama’an jihar na kin siyan garin Amala daga kamfanin ‘Amala Delicacy’ wanda sune masu hada garin Amala, kuma suna gargadin sauran jama’a akan haka.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan lafiyan jihar, Rafiu Isamotu yace an dauki matakan tabbatar da gaskiyar abinda ya kashe su, kuma ya roki jama’a da daina yada jita jita. Inda yace an dade ana cin Amalan, amma ba’a samu mutuwa ba, tana iya yiwuwa daga miyar ne, inji shi.

Kwamishinan yace sun aika da kwararru da zasu gudanar da gwaje gwaje akan garin Amalan don gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng