Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Zulum Ta Yi Wa Ma’aikata Sha Tara Na Arziki, an Samu Ƙarin Bayani

Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Zulum Ta Yi Wa Ma’aikata Sha Tara Na Arziki, an Samu Ƙarin Bayani

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya bayar da umarnin a saki naira biliyan 2.1 don raba wa ma'aikata da 'yan fansho na jihar
  • Za a fitar da kudin ne domin rage wa ma'aikata da iyalan wadanda suka mutu a jihar radadin tsadar rayuwar da ake fuskanta a kasar
  • Tuni dai gwamnatin Borno ta fara rabon hatsi ga gidaje 100,000 a Maiduguri da kewaye domin rage radadin matsin tattalin arziki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Borno - Gwamnatin Borno ta amince da fitar da naira biliyan 2.1 nan take domin biyan kudaden hutun ma’aikata da kuma giratuti na masu ritaya.

Shugaban ma’aikatan jihar Borno, Mallam Fannami ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Maiduguri, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na NAN ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Babban labari: Gwamnatin Najeriya ta cafke jami'an manhajar Binance, an samu ƙarin bayani

Gwamna Zulum ya ware naira biliyan 2.1 don biyan hakkokin ma'aikata
Gwamna Babagana Zulum ya raba kudi a jihar Borno. Hoto: @ProfZulum
Asali: Twitter
“La'akari da halin da ma’aikatan gwamnati ke ciki, Gwamna Babagana Zulum ya bayar da umarnin a saki naira biliyan 2.1 don magance illar cire tallafin man fetur,”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- In ji Mallam Fannami.

Yadda gwamnatin Zulum ta kasafta kudin da ta fitar

Ya kara da cewa an fitar da kudin ne domin rage wa ma'aikatan gwamnati da iyalan wadanda suka mutu a jihar radadin tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa gwamnatin ta ware naira biliyan daya daga cikin kudin domin biyan kudin giratuti na ma’aikatan gwamnati da suka mutu suna aiki.

An ware naira miliyan 602 domin biyan kudin hutu da kuma naira miliyan 500 don biyan giratuti ga ma’aikatan ma’aikatar hadin kan kananan hukumomi.

Gwamnati ta fara rabon hatsi ga gidaje 100,000

Kara karanta wannan

Jerin ministocin Tinubu 12 da suka fi kowa kokari bayan binciken ayyukansu

"Gwamna na rokon ma’aikatan gwamnati da su kara hakuri da fahimta a kokarin da ya ke na magance matsalolin da suke da su daga abin da gwamnati ke da shi."

- Mallam Fannami.

Tuni dai gwamnatin Borno ta fara rabon hatsi ga gidaje 100,000 a Maiduguri da kewaye domin rage radadin matsin tattalin arziki, rahoton Leadership.

Zulum ya raba kayan abinci na naira miliyan 225 a Bama

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Babagana Zulum ya raba wa al'ummar yankin Bama da ke jiharsa ta Borno kayan abinci.

Kayan abincin an ƙiyasta kudin su ya kai naira miliyan 225, kuma an raba su ne ga al'ummar yankin don rage masu radadin tsadar abinci da matsin tattalin arziki da suke fuskanta.

Mafi akasarin wadanda suka ci gajiyar tallafin, sun kasance iyalan da hare-haren mayakan Boko Haram ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.