Abin da Gwamna Abba Ya Fadawa Malaman Kano da Aka Sa Labule a Fadar Gwamnati

Abin da Gwamna Abba Ya Fadawa Malaman Kano da Aka Sa Labule a Fadar Gwamnati

  • Abba Kabir Yusuf ya hadu da malaman addinin musuluncin jihar Kano a gidan gwamnati da ake ta shirye-shiryen azumi
  • Gwamnan jihar Kano ya yi jan hankali ga malamai magada Annabawa, ya bukaci su gyara masa kure-kuren da ya yi a mulki
  • Abba Gida-Gida ya nuna rashin jin dadinsa ga yadda ake cin mutuncin malamai, kafin a bar taron ya ba masanan shawara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A matsayinsa na Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga malamai su gyara masa idan ya yi kuskure a ofis.

Mai girma gwamnan ya zauna da malaman musuluncin da ke garin Kano a gidan gwamnati kamar yadda ya shaida jiya a shafinsa.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Sai an gyara yadda Hukumar Hisbah take aiki a Kano inji Abba Gida Gida

Abba Kabir Yusuf
Gwamna tare da malaman musulunci a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamna Abba ya zauna da malaman Kano

Daily Nigerian ta rahoto cewa malaman masallatan Juma’a suna cikin wadanda aka zauna da su bayan dawowar gwamnan daga ketare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makasudin zaman kamar yadda Mai girma Abba Kabir Yusuf ya fada shi ne neman albarkar malamai sannan ya bukacin taimakonsu.

Kano: Watanni 9 a mulkin Abba Gida Gida

Mai girma Gwamnan yana son jin ra’ayin malaman addini game da watanni tara da ya yi a ofis bayan doguwar shari'a da aka yi a kotu.

A duk inda ya yi wani kuskure ko ake da wata shawara da za a ba gwamnatinsa, gwamna Abba Yusuf ya bude kofa domin daukar gyara.

An rahoto Abba yana cewa hakan zai taimaka wajen dawo da martaba da darajar Kano sa'o'i bayan an hana yin nadin sarauta a Bichi.

Kara karanta wannan

Gwamna zai ɓamɓaro aiki, ya nemi a binciki abin da aka kashe a gyaran lantarki tun 1999

Kano: Za a inganta malamai da masallatai

Legit ta samu labari gwamnatin NNPP ta nuna ana kokarin kara albashin da ake biyan malamai kuma za a koma biyan kudin ta banki.

Ba a nan kurum Abba ya tsaya ba, ya shaida cewa za su gyara duka masallatan Juma’a na garin Kano domin daga darajar musulunci.

Gwamna ya ce tarbiya tayi rauni a jihar Kano

A taron da aka yi, gwamnan ya koka a kan yadda tarbiyya ta tabarbare a jihar Kano, ya ce aikinsu ne su taimaki malamai wajen gyara.

Ganin mawuyacin halin da aka shiga, Abba ya ce zunuban da ake aikatawa suna cikin sanadi, yake cewa wajibi ne mutane su tuba.

A lokacin da ya koka da cin mutuncin malamai, gwamna ya yi kira ga malaman su guji taba ‘yan siyasa, su tsaya wajen koyar da addini.

Abba ya soki aikin jami'an Hisbah

A zantawarsa da malamai, ana da labari cewa gwamnan jihar Kano ya nuna takaici a kan yadda Hisbah ta ke aikinta babu bin doka.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu yayi maganar shirin kifar da shi, Sojoji su karbi Gwamnatin Tarayya

Abba Kabir Yusuf bai ji dadin ganin ana dukan wadanda ake zargi ba, ya ce bai dace a ci zarafin jama’a wajen kokarin gyara al'umma ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng