Akwai matsala: Sai An Gyara Yadda Hukumar Hisbah Take Aiki a Kano inji Abba Gida Gida

Akwai matsala: Sai An Gyara Yadda Hukumar Hisbah Take Aiki a Kano inji Abba Gida Gida

  • Abba Kabir Yusuf ya yiwa hukumar Hisbah gyara a kan yadda ta ke gudanar da ayyukanta domin magance barna a Kano
  • Gwamnan jihar Kano ya shaida haka ne a lokacin da ya hadu da malamai a fadar Gwamnati daga dawowarsa daga Saudiyya
  • Kalaman sun jawo surutu ganin yadda ake ta caccakar Hisbah da kuma abubuwan da suka faru game da Murja Kunya

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano yana ganin akwai kura-kurai a yadda wasu hukumomi suke gudanar da aikinsu.

Gidan rediyon Freedom ta rahoto Mai girma Abba Kabir Yusuf yana kokawa kan yadda jami’ai kan ci zarafin wadanda ake zarfi da laifi.

Hisbah
Gwamna ya soki aikin Hisbah a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf/Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim (Daurawa)
Asali: Facebook

Kano: Gwamna Abba ya tabo Hisbah

Gwamnan ya nuna tun farko sun dauko wanda ya dace ne, suka ba shi rikon hukumar, amma ya ce wajibi a kare hakki.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba ya fadawa malaman Kano da aka sa labule a fadar gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ana duka da gora, suna gudu ana bi, ana tadiye kafafunsu, ana jefa su a cikin Hilux."
"Wannan muna ganin kuskure ne babba, ka rungumo matashiya ko matashi, ka jefa shi kamar akuya a cikin Hilux."
"Hisbah hukuma ce wanda muka dauke ta da martaba, kuma muka debo Bayin Allah wadanda muka san za su iya, muka ce ga amanar al’ummar jihar Kano."

- Abba Kabir Yusuf

Abba ya ba hukumar Hisbah shawarwari

A taron da ya yi da malamai a gidan gwamnati, Abba Yusuf ya yi kira ga hukumomin da ke lura da tarbiyya da su yi abin da ya kamata.

Gwamnan Kano ya kuma bukaci shawarwarin kwarai da hadin-kai da irinsu Hisbah da ke karkashin jagorancin Aminu Ibrahim Daurawa.

Kwanakin baya Hisbah ta ziyarci wasu wurare domin toshe badala a Kano, bidiyon wannan aiki ne ya tada hankalin gwamna Abba.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata, sun fito zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga a jihar Arewa

Abba bai ji dadin ganin yadda dakarun Hisbah suka shiga dakunan dalibai ba, ya ce sai an bi a sannu ka da matasan Kano su kangare.

Idan za a yi aiki, gwamnan ya ce a hada da 'yan sanda, DSS, NSCDC, sai a damkawa hukuma.

"Wannan ba daidai ba ne" inji Mazaunin Kano

Legit tayi magana da Mustapha Abdulrauf Tukur wanda yana cikin global shapers community ta reshen Kano domin jin ra’ayinsa.

"Ba na jin yanzu ne lokacin da gwamnati zata soki wani aiki da Hisbah tayi in dai ba da wata a ƙasa ba, musamman duba da barazanar da hisbar ta fuskanta a ‘yan kwanakin nan daga ciki da waje."
"Har yanzu ba fa gamsasshiyar amsa kan abinda ya wakana a kan dambarwar hisbah ɗin da wata da kotu ta kai kurkuku bayani ya so canzawa."

- Mustapha Abdulrauf Tukur

Injiniya Mustapha Abdulrauf Tukur ya ce kamar babu hadin-kai tsakanin gwamnati da hukumar bayan an yi dambawar Murja Kunya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 2 sun saduda yayin da suka mika wuya ga 'yan banga a Arewa, sun fadi dalili

“Hakan kuma babbar barazana ce kan manufar gyaran da aka sa a gaba. Allah ya kyauta.”

- Mustapha Abdulrauf Tukur

APC ta soki Gwamna a kan taba Hisbah

A wani rahoton, an ji jam’iyyar APC tana cewa kalaman gwamnan sun ba ta mamaki.

Idan za a tuna, Sheikh Aminu Daurawa ya rike mukamin nan a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, daga baya ya ajiye kujerar.

Dawowar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Bayan an rantsar da gwamnatin NNPP sai aka ji labari Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya maido Sheikh Aminu Daurawa kujerar.

Daurawa ya sake karbar shugabancin hukumar Hisbah ta Kano a karo na biyu saboda ya ga gaske gwamnatin za ta yi aiki da gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng