An Shiga Jimami Bayan Tsohon Minista a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Majalisar zartarwa ta yi alhinin rashin tsohon Ministan ilimi a Najeriya, Farfesa Fabian Osuji a yau Alhamis
- Marigayjn ya rasu a jiya Laraba 28 ga watan Faburairu bayan ya dawo daga kasar Amurka a ranar Asabar
- Fabian ya rike mukamin Ministan ilimi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan ilimi a Najeriya, Farfesa Fabian Osuji ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya.
Marigayin, Osuji ya rasu ne a jiya Laraba 28 ga watan Faburairu ya na da shekaru 82 a duniya, cewar The Nation.
Yaushe marigayin ya rike mukamin Minista?
Wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar cewa Osuji ya dawo daga Amurka a ranar Asabar inda ya yi jinya kan wata cuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fabian ya rike mukamin Ministan ilimi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.
An haifi marigayin a ranar 20 ga watan Janairun 1942 a jihar Imo inda ya halarci makarantar firamare da sakandare a jihar.
Daga bisani ya tafi Jami'ar Najeriya ta Nsukka a jihar Enugu da kuma Jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo, The Source ta tattaro.
Farfesa ya taba aiki a Jami'ar St. John da ke birnin New York a Amurka daga shekarar 1997 zuwa 1999.
Martani Gwamnatin Tarayya kan rasuwar Farfesan
Majalisar zartarwa ta FEC ta yi alhinin mutuwar Farfesan wanda ya rasu a jiya Laraba e 28 ga watan Faburairu.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume wanda ya yi magana a madadin Majalisar ya bayyana rashin a matsayin mai wuyar cikewa.
Daraktan yada labaran Akume, Segun Imohiosen shi ya bayyana haka a yau Alhamis 29 ga watan Faburairu.
Akume ya ce tabbas an yi babban rashi na mutum mai ilimi wanda ya ba da gudunmawa sosai a bangarori da dama na kasar.
Jarumin fina-finan Nollywood ya rasu
Kun ji cewa fitaccen jarumin fina-finan a Najeriya ya rasu bayan fama da doguwar jinya a jihar Ogun.
Marigayin Jimi Solanke ya rasu ne bayan jeka-ka-dawo da aka ta yi da shi daga asibiti zuwa gida tun a watan Disambar 2023.
Asali: Legit.ng