Duk da Durkusar da Najeriya, an Bayyana Emefiele a Matsayin Mafi Kwarewa a CBN, Akwai Dalilai
- Duk da zarge-zargen da ke kan tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya samu yabo daga wata kungiyar a Najeriya
- Kungiyar, Agbor Stakeholders Forum ta ce ba a taba samun shugaban bankin da ya kawo sauye-sauye a fannin tattalin arziki kamar shi ba
- Sakataren yada labaran kungiyar, Kanene Kachikwu shi ya bayyana haka inda ya ce binciken Emefiele siyasa ce
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - An bayyana tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele a matsayin wanda ya fi kowa kwarewa.
Wata kungiyar mai suna Agbor Stakeholders Forum ita bayyana haka inda ta ce ba a taba samun kamarsa ba a shugabancin bankin.
Menene kungiyar ke cewa kan Emefiele?
Sakataren yada labaran kungiyar ta kasa, Kanene Kachikwu shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Emefiele shi ne na farko wanda ya kawo sauyi a fannin tattalin arzikin Najeriya a lokacin da ya ke gwamnan bankin.
Kungiyar ta ce ganin yadda tallafin arziki ya ke a kasa da shekara daya na Tinubu ya tabbatar da wakilci nagari da Emefiele ya yi a lokacin mulkin Buhari.
Ta kara da cewa Emefiele ya yi kokarin tsamar da kasar har sau biyu yayin da ta shiga matsin tattalin arziki, Vanguard ta tattaro.
Martanin kungiyar kan tuhumar Emefiele
Har ila yau, ta ce wannan bincike da ake yi kan Emefiele kawai siyasa ce saboda sun gaza farfado da tattalin arzikin ƙasar.
A cewarta:
"Kamar yadda muka sha fada, laifin Emefiele shi ne sauya fasalin naira wanda Buhari ya yi don rage yawan kashe kudade a zabe.
"Ya so ya inganta harkar zaben da aka gudanar a watan Faburairun 2023 amma aka samu matsala.
"Muna alfahari babu wani shugaban bankin da ya kawo sauye-sauye a CBN kamar yadda Emefiele ya yi a lokacinsa."
Tinubu zai haramta Kiripto
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya na ta kokarin dakile harkar Kiripto a Najeriya ganin yadda harkokin ke da tasiri a matsalar tattalin arzikin kasar.
Wannan na zuwa ne bayan kame wasu shugabannin Binance a Abuja yayin da suka zo don tattauna kan matsalar.
Asali: Legit.ng