Kalaman Akpabio Kan Emefiele Sun Jefa shi Cikin Babbar Matsala

Kalaman Akpabio Kan Emefiele Sun Jefa shi Cikin Babbar Matsala

  • Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya yi wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, barazana kan ɓata masa suna
  • Ta bakin lauyansa Emefiele ya buƙaci shugaban majalisar dattawa da ya nemi afuwa ko kuma ya fuskanci shari’ar ɓata suna ta naira biliyan 25
  • Akpabio a ranar Lahadin da ta gabata ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gaji tattalin arziƙi wanda Emefiele ya lalata a lokacin yana gwamnan CBN

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya buƙaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya biya shi naira biliyan 25 a matsayin diyya, bisa zargin ɓata masa suna.

A ranar Lahadin da ta gabata, Akpabio ya ce zarge-zargen da ake yi wa Emefiele na da yawa wanda gwamnatin tarayya ba ta san irin tuhume-tuhumen da za ta yi masa ba.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa ya tona asirin masu ɗaukar nauyin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohi 4

Emefiele ya taso Akpabio a gaba
Emefiele ya bukaci Emefiele ya biya shi N25bn Hoto: Godwin Emefiele, Godswill Akpabio, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Shugaban majalisar dattawan ya kuma ɗora laifin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar nan kan manufofin tsohon gwamnan na CBN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wasikar mai ɗauke da kwanan watan 19 ga watan Fabrairu wacce jaridar TheCable ta gani a ranar Laraba, Emefiele ya aike da gargaɗi ga shugaban majalisar dattawan.

Me Emefiele yake buƙata a wajen Akpabio?

Matthew Burkaa, lauya ga Emefiele, ya ce idan Akpabio ya kasa biyan kuɗaɗen da aka ambata da neman yafiya, tsohon gwamnan na CBN zai ɗauki "matakin da ya dace", rahoton Leadership ya tabbatar.

A cewar lauyan, kalaman Akpabio na nuni da cewa Emefiele babban mai laifi ne wanda matakan da ya ɗauka su ne suka jawo wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Lauyan ya yi iƙirarin cewa maganar idan aka fassara ta a zahiri, tana nufin abu ɗaya ne, kuma hakan ya ɓata sunan wanda yake karewa, Emefiele.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya caccaki Tinubu, ya fadi wani babban kuskure da yake yi

Emefiele ya kuma bayyana cewa kalaman da Akpabio ya yi na kawo cikas ga gaskiya da ƴancin cin gashin kai na kotu kuma hakan na da illa ga shari’ar da ake yi masa a kotu.

An Bankaɗo Sabuwar Badaƙala a CBN

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta bayyana cewa an gano wasu kuɗaɗe da suka kai $8bn da aka fitar a bankin CBN.

Ƙungiyar ta ce Odita Janar na ƙasa ya umarci bankin CBN da ga fito ya yi bayanin kan dalilin da ya sanya aka fitar da kuɗaɗen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng