Matar Aure Ta Shiga Damuwa Yayin da Mijinta Ya Yi Gum Bayan Ya Kama Ta Tana Ci Masa Amana Tun 2023

Matar Aure Ta Shiga Damuwa Yayin da Mijinta Ya Yi Gum Bayan Ya Kama Ta Tana Ci Masa Amana Tun 2023

  • Auren wasu ma'aurata yana tangal-tangal bayan mijin ya kama matarsa tana ci masa amana amma ya ki cewa uffan ko ya tunkare ta
  • Cike da damuwa, matar ta kai karar mijin nata wajen iyayensa da kuma fasto dinsu domin su shiga tsakani
  • A cewar wata lauya mai kare hakkin 'dan adam, mutumin ya ci gaba da gudanar da harkokinsa a matsayin miji ta fuskanci kudi tun faruwar lamarin kamar dai babu komai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matar aure ta yi karar mijinta a wajen iyayensa saboda ya ki cewa komai tun bayan da ya kama ta tana cin amanarsa.

Bolanle Cole, wani lauya mai kare hakkin 'dan adam, wanda ya bada labarin a shafinsa na X, ya ce wani abokin harkarsa ya kama matarsa tana cin amana sannan ya ajiye abin a matsayin sirri.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Mutanen Abuja sun koma ga awara a madadin nama

Matar aure ta shiga damuwa bayan mijinta ya gano tana ci masa amana
Matar Aure Ta Shiga Damuwa Yayin da Mijinta Ya Yi Gum Bayan Ya Kama Ta Tana Ci Masa Amana Tun 2023 Hoto: Robin Gentry, Juanmonino
Asali: Getty Images

Maimakon haka, sai mijin ya daina cin abinci a gida sannan ya kauracewa kwanciya da ita amma dai bai daina dauke mata dawainiyar kudi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ta ga cewa mijin na sane da cin amanar da ta yi masa, sai matar ta shiga damuwa yayin da ta gaza gane dalilinsa na kwantar da hankali kan lamarin.

Matar ta sako fasto cikin lamarin

Bolanle ya kara da cewar matar ta kuma yi karar mijin nata a wajen fasto dinsu tare da iyayensa. Mijinta ya fada masu cewa su tambayeta abin da ta yi.

Bolanle ya ce mijin ya gano cin amanar da matar tasa ta yi tun a watan Oktoban 2023. Ya rubuta:

"Wani abokin harka ya kama matarsa tana ci masa amana sai ya yanke shawarar boye abin sannan ya ki sanar da matar amma ya yanke shawarar daina cin abinci a gida.

Kara karanta wannan

Yadda ma'aikaciyar banki ta ajiye aikinta na shekaru 13, ta kama sana'ar da ke kawo mata kudi kullun

"Babu kwanciyar aure ko wani abu tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata amma yana daukar dawainiyar gidansa.
"Matar ta zauce, ta gaji, ta shiga damuwa domin bata san dalilin sauya dabi'un da mijinta ya yi.
"Ta yi karar mutumin wajen iyayensa, fasto dinsu, mutumin ya bukaci da su tambayeta abin da ta yi."

Jama'a sun yi martani

@AdeduluE ya ce:

"Mataki mai hikima. Irin mutum mai hankali haka."

@ebubec1 ya ce:

"Mutumin wawa ne, ya sauya wasiyyarsa. Toh idan matar ta kashe shi a cikin baccinsa fa? Babu amfanin boyewa, kawai ka ci gaba da harkokinka."

@belovethchild7 ya ce:

"Ba za ta taba fadin gaskiya ba sai dai idan ka nuna mata shaida na gaske, Mata suna da wuyar sha'ani."

@Raph19406818 ta ce:

"Mutumin nan n da hatsari, ki gudu faaaa."

Amarya ta sharbi kuka ranar aurenta

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata amarya ta cika da bakin ciki saboda mai daukar hoton da ta dauko ya ki hallara domin daukar su hotuna a rana mafi girma da muhimmanci a gareta.

A wani bidiyo da ya yadu, an gano 'yan uwa da abokan arziki kewaye da amaryar yayin da take hawayen bakin ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng