Yadda Aka Damke Shugabannin Kamfanin Binance Daga Kasar Waje a Yunkurin Karya Dala
- Shugabannin kamfanin Binance da suka zo Najeriya da nufin tattaunawa da gwamnatin tarayya sun iso da kafar hagu
- Ana zargin jami’an tsaro sun tsare wadannan mutanen biyu bayan an samu rashin jituwa a zaman da aka yi da su a Abuja
- Gwamnatin Najeriya ta bukaci wasu bayanan shekara da shekaru wanda shugabannin Binance ba su ba hukuma ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Gwamnatin Najeriya ta damke wasu shugabanni biyu na kamfanin Binance a yunkurin da ake yi na karya farashin Dala a kasar.
Rahoton da Premium Times ta kadaita da shi ya ce wadannan manyan jami’ai suna tsare a Abuja kwana guda daga zuwansu Najeriya.
An kama shugabannin Binance a Najeriya
Shugabannin na Binance sun hau jirgi zuwa kasar nan ne da nufin a tattauna da gwamnati yayin da aka kakabawa kafarsu takunkumi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mahukuntan Najeriya suna zargin cewa kamfanin na Binance yana bada gudumuwa wajen tashin da Dalar Amurka take yi a kasuwar canji.
‘Yan canji suna kuka da kafofin yanar gizon, ana zarginsu da bada farashin kudin ketaren da ba na gaskiya ba, hakan yana karya Naira.
Zaman jami'an Binance da ONSA a Abuja
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa a ranar Lahadi wadannan jami’ai suka iso, zuwa Litinin suka zauna da jami’ai daga ofishin NSA.
Sai dai shugabannin na Binance ba su amince da bukatun mai ba shugaban kasa shawarar tsaro ba, ba a cin ma matsaya a zaman ba.
Binance sun saba dokokin Najeriya?
An zargi kamfanin Binance da saba dokoki da yin kasuwanci ba tare da cika sharuda ba.
Gwamnati ta bukaci a fito mata da bayanan cinikin Naira da aka yi a Binance na shekaru bakwai, amma jami’an sun ki bada hadin-kai.
Binance: Za a tsare mutanen kasar waje
Nan take gwamnatin Bola Tinubu ta nemi izinin kotu a fara tsare su na kwanaki 12.
The Nation ta ce wadannan bayin Allah da aka tsare daga ketare suke. Ana tunanin a cikinsu akwai Ba Amurke da bature 'dan Fakistan.
A daidai lokacin da EFCC ta ke gudanar da bincike, wadannan mutane suna rufe a wani gidan saukar da baki a kusa da ofishin NSA.
CBN ya haramta Bitcoin
A shekarun baya ne rahoto ya zo cewa gwamnan babban bankin Najeriya ya sake jaddada haramcin aiki da kudin yanar gizo na bitcoin.
Bayan nan daga baya gwamnati ta sa an toshe kafofin Forextime, OctaFX, Crypto, FXTM, Coinbase da Kraken da ake ciniki ta yanar gizo.
Asali: Legit.ng