Gwamna Zai Ɓamɓaro Aiki, Ya Nemi a Binciki Abin da Aka Kashe a Gyaran Lantarki Tun 1999
- Gwamna Hope Uzodinma yana so a fara bincike a kan yadda aka shiga matsalar wutar lantarki bayan an narka makudan kudi
- Daga 1999 zuwa 2007, gwamnan ya ce sama da $13bn aka kashe domin gyara wuta, amma har gobe babu wuta a Najeriya
- Mai girma Hope Uzodinma ya koka da yadda lamarin ya tabarbare bayan shekaru 25, ana cin baya maimakon a yi gaba a kasar
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Enugu - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya bukaci gwamnatin Najeriya ta binciki biliyoyin da aka kashe domin gyara lantarki.
Mai girma Hope Uzodinma yana so a fara binciken tun daga 1999 da aka dawo mulkin farar hula, Premium Times ta kawo rahoton.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a ranar Litinin sa’ilin da aka kaddamar da wani shiri domin ‘yan kasuwan yankin Kudu maso gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi taro ne a tsohon gidan gwamnati da ke garin Enugu wanda ya samu halarcin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Kamfanin NDPHC wanda yana cikin wadanda kwamitin Oronsaye zai taba ya shirya taron da nufin inganta lantaki a kudu ta gabas.
Gwamnati ta kashe kudin wuta a iska?
Da ya tashi jawabi, gwamnan Imo ya ce abin takaici ne a ce gwamnatoci sun kashe biliyoyin daloli amma har yau ba a samu wuta ba.
"A 1998, Najeriya ta na samar da fiye da megawatt 6, 000 lantarki. Daga 1999 zuwa 2007, gwamnati ta kashe fiye da $13bn domin inganta harkar."
"Zuwa 2024, babu wuta a 78% na gidaje da kamfanonin Najeriya, shakka babu akwai babbar matsala."
"Akwai bukatar a yi cikakken binciken matakan da aka dauka a baya – inda aka yi daidai da inda aka yi kuskure."
- Hope Uzodinma
25% suke samun lantarki a Najeriya
The Nation ta rahoto Uzodinma yana kokawa cewa 75% na kasuwancin kudu maso gabas ya mutu duk da mutanen suna da kokarin nema.
Uzodinma ya ce akwai a arziki a yankin amma a banza, kuma ya ce babu adalci a ga laifin Bola Tinubu wanda ya hau mulki a shekarar bara.
Gwamnati ta cire tallafin fetur
An ji labari Babachir David Lawal ya yi watsi da Bola Tinubu wanda a baya yake tare da shi, ya zargi gwamnatin APC da wahalar da mutane.
Babachir David Lawal ya soki yadda aka jawo fetur ya tashi ba tare da an yi koyi da irinsu Cif Olusegun Obasanjo da Janar Sani Abacha ba.
Asali: Legit.ng