An fara: EFCC ta kaddamar da bincike kan $16bn na kudin wutan lantarki da Obasanjo yayi

An fara: EFCC ta kaddamar da bincike kan $16bn na kudin wutan lantarki da Obasanjo yayi

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta kaddamar da binciken kan kudin $16 billion da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, yayi ikirarin kashewa wajen samar da wutan lantarki a Najeriya.

A ranan Talata, shugaba Muhammadu Buhari ya soki gwamnatin Obasanjo kan almubazzarancin da sukayi da kudin al'umma. Amma tsohon shugaban kasan ya musanta hakan.

Game da cewar jaridar The Nation, an nada kwamiti a hukumar EFCC da zasuyi bincike cikin wannan abu.

Rahoton ya bayyana cewa da yiwuwan a gayyaci tsaffin ministoci biyu, tsaffin ma'aikatan hukumar NEPA (PHCN), ma'aikatan hukumar Niger Delta Power Holding Company (NDPHC), da kuma duk wanda yan kwamitin suka bukaci gani.

"Muna dubi cikin zargin da abubuwan da suka tattari ayyukan. Zamu gudanar da bincike sama-sama domin sanin yadda akayi ayyukan."

KU KARANTA: Rundunar sojojin Najeriya ta 7 dake yaki da Boko Haram a Maiduguri tayi sabon shugaba

“Wannan bincike zai taimaka wajen sanin nawa aka kashe. an samu sabani kan kudin da aka kashe, shin $16 billion, $13.278 billion, $10.3 billion, $8.4 billion da $8.55 billion

"Wannan bincike ba wai bita da kulli ake yiwa tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ba ko wani. Akwai bukatan muyi dubi cikin takardu."

A shekarar 2008, kwamitin Elumeli, tace an kashe kimanin $13 billion kan wutan latarki daga 1999 zuwa 2007.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel