Jerin Ministocin Tinubu 12 da Suka Fi Kowa Kokari Bayan Binciken Ayyukansu
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kasance a sama a jerin Ministocin da suka fi kowa kokari a gwamnatin Bola Tinubu.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Wannan na zuwa ne bayan an fitar da jerin Ministoci 12 da suka fi kowa kokarin tun bayan hawan wannan gwamnati.
Jerin Ministocin da suka yi fice
Yayin taron majalisar zartarwa a Abuja, rahoton ya bayyana himmatuwar ministocin wurin aiki tukuru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta leko rahoton inda ta jero muku Ministocin kan kokarin da suka yi.
1. Nyesom Wike
An yabawa Wike kan kirkirar hukumar ma'aikatan Abuja da umarni ga 'yan kwangila su kammala aikin jirgin kasa.
Sauran sun hada da samar da tsaro da kudin shiga da kuma hanyoyi a birni Abuja, cewar The Nation.
2. Wale Edun
Edun ya samu yabo wurin tabbatar da inganta tattalin arzikin kasar bayan cire tallafin mai, cewar The Guardian.
Ministan kudade da tattalin arziki ya samar da hanyoyin kudin shiga ga gwamnatin da kuma kokarin yaye talauci ga 'yan kasa.
3. Farfesa Ali Pate
Ali Pate ya samu yabo wurin tabbatar da inganta harkar lafiya da samar da riga-kafi ga al'umma., PRNigeria News ta tattaro.
4. Olabunmi Tunji-Ojo
Ministan harkokin cikin gida ya yi kokarin kawar da fiye da matsalar fasfo dubu 200 a 'yan makwanni bayan nada shi ministan.
5. Mohammed Idris
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a ya kasance na biyar a jerin bayan yawan tarurruka kan abin da ya shafi Najeriya da kuma wayar da kan jama'a.
Sauran Ministoci bakwai din sun hada da:
6. Adegboyega Oyetola - Ministan Albarkatun Ruwa
7. Ohanenye Uju Kennedy - Ministar Harkokin Mata
8. Dele Alake - Ministan Albarkatun Kasa
9. Doris Uzoka-Anite - Ministar Masana'antu
10. David Umahi - Ministan Ayyuka
11. Festus Keyamo - Ministan Harkokin Jiragen Sama
12. Bosun Tijani - Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani
Tinubu zai fara biyan matasa alawus
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya amince da fara biyan matasa marasa aikin yi alawus saboda halin da ake ciki.
Wannan na zuwa ne yayin da matasan da sauran jama'ar kasar ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng