NNPCL Ya Faɗi Lokacin da Zai Kawo Ƙarshen Wahalar Man Fetur a Najeriya
- Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, Mele Kyari ya tabbatar wa ƴan ƙasar cewa nan da shekaru 10 za a daina wahalar fetur
- Mele Kyari ya ce kamfanin NNPCL ya saka hannu jari a bankin makamashi na Afrika don tabbatar da dorewar kudaden ayyukan man
- Ya bayyana hakan ne a wajen wani bikin bude taron kasa da kasa na makamashin Najeriya karo na bakwai da aka gudanar yau a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya tabbatar wa ‘yan kasar cewa zai kawo karshen wahalar man fetur a kasar nan da shekaru 10 masu zuwa.
Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau Talata a wajen bikin bude taron kasa da kasa na makamashin Najeriya karo na bakwai da aka gudanar a Abuja.
Wa'adin da NNPC ya dauka don wadatar da fetur
Mele Kyari ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki a taron kudurin kamfanin na yin aiki tare da su don rufe gibin makamashi da aka samu da kuma wadatar da shi ga ‘yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPC, Olufemi Soneye ya fitar, kamar yadda The Punch ta gani, Kyari ya ce:
"Daga dukkan alamu, dukkan matsalolin karancin makamashi a kasar za su kare nan da shekaru 10 masu zuwa."
NNPC ya saka hannun jari a bankin makamashi na Afirka
Kyari ya ce NNPC ne babban abokin hulda ga daukacin kamfanonin da ke hako mai a Najeriya, kuma ya ba da tabbacin cewa zai samar da inganci da dorewar makamashi don amfanin ‘yan Najeriya.
Ya kuma bayyana aniyar kamfanin na saka hannun jari a bankin makamashi na Afirka a matsayin hanyar tabbatar da dorewar kudaden ayyukan makamashi a Afirka.
Mayan masu ruwa da tsaki da suka halarci taron
Daily Post ta ruwaito cewa taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki, ciki har da sakatare-janar na kungiyar kasashe masu fitar da arzikin man fetur, Haitham al-Ghais.
Sauran sun hada da; Babban sakataren kungiyar masu samar da man fetur ta Afirka, Omar Farouk Ibrahim da Karamin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri.
Sai kuma ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris Malagi, wanda ya wakilci shugaba Bola Tinubu.
Litar fetur ta kai N1,000 a wajen ƴan bumburutu
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa ƴan bumburutu sun fara sayar da litar fetur akan naira 1,000 a wasu sassa na birnin Legas da Abuja da jihar Ogun.
Kamar yadda rahoton ya nuna, tun bayan da kungiyar direbobin dakon fetur suka ayyana shiga yajin aiki man ya katse, wanda ya jawo dogon layi a gidajen mai.
Amma daga bisani direbobin sun janye daga yajin aikin bayan ganawa da gwamnati, sai dai duk da hakan, ƴan kasuwa sun ce NNPC ya daina sayar masu da fetur.
Asali: Legit.ng