Labari Mai Dadi: An Bayyana Lokacin da Farashin Man Fetur Zai Sauka a Najeriya

Labari Mai Dadi: An Bayyana Lokacin da Farashin Man Fetur Zai Sauka a Najeriya

  • Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa a shekarar 2024 farashin man fetur zai sauka
  • Cardoso ya bayyana cewa farashin zai yi ƙasa ne da zarar matatun man fetur masu zaman kansu da na gwamnati sun fara aiki
  • Gwamnan na CBN ya kuma bayyana cewa za a samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a cikin shekarar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa farashin man fetur zai daidaita a wannan shekarar.

Gwamnan na CBN ya bayyana cewa farashin zai daidaita ne da zarar matatun mai na gwamnati da masu zaman kansu sun fara aiki, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya damfari mabiyansa $1.3m, ya bayyana wanda ya ba shi umarnin yin hakan

Gwamnan CBN ya ce farashin man fetur zai sauka
Cardoso ya yi nuni da cewa a 2024 za a samu raguwar farashin man fetur Hoto: @dipoaina1
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, a wajen ƙaddamar da rahoton (NESG 2024) kan tattalin aziƙi a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me raguwar farashin man fetur zai haifar?

Cardoso ya ce raguwar farashin da ake sa rai, yana da tasiri sosai a sassa daban-daban, inda zai ƙara ba da gudunmawa sosai ga tattalin arziƙin ƙasar nan.

Jaridar The Punch ta ambato Cardoso yana cewa hauhawar farashin kayayyaki zai yi ƙasa zuwa kaso 21.4% a wannan shekarar ta 2024.

Yayin da matatar man Dangote tuni ta fara aikin tace man fetur, ana sa ran za a fara tace man fetur a matatar mai ta Port Harcourt, kowane lokaci daga yanzu.

Cardoso ya ce CBN da ma’aikatar kuɗi da kuma kamfanin NNPCL sun haɗa kai don tabbatar da cewa an mayar da dukkan kuɗaɗen waje da ake shigowa da su zuwa CBN domin bunƙasa kuɗaɗen ajiya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan APC da NNPP, bayanai sun fito

Ya bayyana Naira wacce ake canjawa kan N1,370 da dalar Amurka ɗaya, a matsayin wacce ba hakan ba ne haƙiƙanin darajarta.

Ya Batun Ƙara Kuɗin Man Fetur?

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), ya fito ya yi magana kan batun ƙara farashin man fetur da ake ta jita-jita a kansa.

Kamfanin wanda ya tabbatar da cewa batun dawo da tallafin man fetur ba gaskiya ba ne, ya kuma tabbatar da cewa babu shirin ƙara farashin kuɗin man fetur ɗin daga N620 zuwa N1200 a gidajen mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel