Gwamnatin Shugaba Buhari za ta kammala aikin da aka yi shekaru 42 ana jira a Najeriya
Olamilekan Adegbite ya yi alkawari za a karkare aikin kamfanin Ajaokuta
Ministan ya ce kamfanin da za su fara wannan aiki suna nan zuwa Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta ce annobar Coronavirus ta jawo aka gaza fara aikin
Ministan karafuna na kasa, Olamilekan Adegbite, ya ce kamfanin Ajaokuta zai fara aiki kafin karshen wa’adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
NAN ta ce Olamilekan Adegbite ya shaida wa manema labarai wannan a wajen wani taro a garin Abuja.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta yi kokari wajen kawo kamfanin kasar Rasha da za su soma aiki domin ganin yiwuwar karasa gagarumin kwangilan.
A cewar Ministan, ya kamata kamfanin ya zo ya fara aiki tun shekarar 2020, amma hakan bai yiwu ba saboda annobar cutar COVID-19 da ta addabi Duniya.
Premium Times ta ce an ci ma yarjejeniya a kan yadda za a babbako da kamfanin a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya hadu da Vladimir Putin.
Kamar yadda Ministan ya fada, Shugaba Muhammadu Buhari ya zauna da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, a kan wannan batu ne tun a shekarar 2019.
Gwamnatin Rasha ta zabi kamfanin TPE ya yi wannan aiki, domin su ne suka gina kamfanin.
Adegbite ya ce makasudin kafa samar da kamfanin shi ne su rika samar da narkakken karfi, sannan aka kafa wani kamfani a Itakpe da zai samar da kwangiri.
Da wannan narkakken karfe ne za a rika gina jiragen sama da kayan karafun mota da sauransu. Hakan kuma zai taikmaka wajen samar da ayyukan yi a kasa.
“Kamfanin karfen Ajaokuta bai taba samar da narkakken karfe ba, tun da aka gina shi – Amma ya kamata mu yi kokarin magance matsalolin da ake fuskanta.”
Dazu kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta fara ganin tasirin Janar Tukur Yusuf Buratai bayan an nada shi Jakada, inda ya taiimaka wajen cafke Sunday Igboho.
Kwanakin baya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Tukur Buratai a matsayin Jakadan Benin.
Asali: Legit.ng