Najeriya ta nada Boss Mustapha da Olamilekan Adegbite su jagoranci kwamitin farfado da ASCL

Najeriya ta nada Boss Mustapha da Olamilekan Adegbite su jagoranci kwamitin farfado da ASCL

- Bayan shekaru 40, ana neman farfado da kamfanin karafan nan na Ajaokuta

- Gwamnatin Buhari ta nada wani kwamiti da zai yi Saiki domin tada kamfanin

Mun samu labari cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta na kokarin dawo da ran babban kamfanin aikin karafunan nan watau Ajaokuta Steel Company Limited (ASCL) da ke jihar Kogi.

A ranar Litinin, 11 ga watan Mayu, 2020, aka nada wani kwamitin da zai dawo da kamfanin aiki. Gwamnatin kasar ta na wannan yunkuri ne domin fadada tattalin arzikin Najeriya.

Wannan kwamiti da aka yi wa suna da Ajaokuta Presidential Project Implementation Team watau APPIT ya na kunshe da mutane 13 kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne shugaban wannan kwamiti. Mustapha ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta na da sha’awar farfado da wannan kamfani.

KU KARANTA: Za mu jawo layin gas tun daga Garin Ajaokuta inji NNPC

Najeriya ta nada Boss Mustapha ya jagoranci kwamitin farfado da Ajaokuta
An ba Boss Mustapha da wasu mutum 12 aikin tada Ajaokuta
Asali: UGC

Ragowar ‘yan kwamitin su ne sakatarorin din-din-din na ma’aikatun ma’adanai da karafa, shari’a, da tattalin arziki. Babban lauyan ma’aikatar shari’a ya na cikin wannan kwamitin.

Ministan ma’adanai da karafa zai zama dayan shugaban kwamitin. Saura su ne: Gabriel Aduda, Vincent Dogo, Farfesa Elegba S.B, Dr. Godwin Adeogba, da kuma shugaban MMSD.

SGF ya ce: “Kamfanin karafunan Ajaokuta ya kasance a dankare na tsawon kusan shekaru 40 ba a iya tabuka komai. Yunkurin da aka yi a baya na farfado da kamfanin ya ci tura.”

“Wannan ya jawo asarar kudin kasar wajen da Najeriya ba za ta iya jurewa ba. Muhimmancin shawo kan wannan kalubale ya sa aka tado wannan kwamiti a daidai lokacin nan.”

Mustapha ya ke cewa za a yi wannan aiki ne ta yarjejeniyar da gwamnati ta shiga da bankin Afrexim da wani kamfanin kasar Rasha a karkashin wasu sharuda da aka kafa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel