Me ya hana Ajaokuta Steel aiki ne, bayan kashe Dala Biliyan 38?

Me ya hana Ajaokuta Steel aiki ne, bayan kashe Dala Biliyan 38?

A da an zaci kamfanin rodi na Ajaokuta zai ishi Najeriya da makwabta, kai har ma saura a duniya su sami sidi, amma shekaru 35 kenan har yanzu ko rodi daya baya fitar ba, kuma ta lashe dala biliyan kusan arbain.

Me ya hana AjaokutaSteel aiki ne, bayan kashe dala biliyan 38?
Me ya hana Kamfanin Ajaokuta Steel aiki?

A da an zaci kamfanin rodi na Ajaokuta zai ishi Najeriya da makwabta, kai har ma saura a duniya su sami sidi, amma shekaru 35 kenan har yanzu ko rodi daya baya fitar ba, kuma ta lashe dala biliyan kusan arbain.

Ajaokuta dai gari ne a kudu da Lokoja, kusa da Okene, a gabar kogin kwara a jihar Kogi. An kafa kanani da zai dinga fidda rodi kirar Steel, wato kare hade da gawayi, wanda yafi kare karfi da juriya, sai dai, ba'a iya cimma burin ba, bayan da gwamnati ta gaza.

Me ya hana AjaokutaSteel aiki ne, bayan kashe dala biliyan 38?
Me ya hana Kamfanin Ajaokuta Steel aiki?

An samar da katafaren kamfanin ne a inda akwai kare da kwal, wato Iron Ore da Coal deposits ne a wurin, wanda ke malale a karkashin kasa, an kuma fara duba yiwuwar kafa kamfanin tun mulkin turawa.

An gama shi a 1984 zamanin mulkin Shehu Shagari, inda aka cimma 98% na aikin, akan dala biliyan 38, saidai kashi 2% da ya rage shima zai ci dala akalla biliyan biyu. Wannan ne ya sanya gwamnatoci suke ta gwanjonsa don kar su kashe wannan kudi, shekari kusa 20 kenan.

DUBA WANNAN: Yan Neja Delta sun yaba wa shugaba Buhari

Obasanjo ya sayar, a 2003, ya dawo ya karbe bayan kasawar kamfanin na Amurkawa, ya sayar wa da Indiyawa, suma suka kasa, Umaru Yar'aduwa ya kwace a 2008, amma kamanin suka garzaya kotu.

Yanzu dai shugaba Buhari ya sake amshe kamfanin a 2016, kuma a maimakon gwanjonshi da yayi niyya, an bashi shawara da ya kammala kashe kudaden da ake bukata, gwamnati ta tafiyar da kamfanin na koda shekara daya ne zuwa goma, sannan ta sayar.

Ba'a dai san ko hakan shugaban yayi niyya ba, ganin har yanzu ba'a waigi kamfanin ba kuma.

Ajaokuta dai zai iya samar da ayyuka dairet 10,000 da indairet 500,000 ga samarin Najeriya. Watau kusan rabin miliyan zasu ci moriyarsa ko da ba a nan suke aiki ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel