Tinubu ya nada Ibrahim Khalil ya zama Darekta, bayan kwanaki 4 ya amince a rushe NEXIM
- Watakila zuwa yanzu Ibrahim Khalil Gaga ya shiga ofis a matsayin sabon darekta mai iko a hukumar NEXIM ta tarayya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin kamar yadda Ajuri Ngalale ya bada sanarwar haka daga fadar Aso Villa
- Ibrahim Gaga yana zama darekta sai aka ji gwamnatin tarayya ta yarda bankin NEXIM da hukumar NEPC su dunkule
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A makon da ya gabata ne aka ji Bola Ahmed ya amince da nadin Ibrahim Khalil Gaga ya zama Darekta a bankin NEXIM.
Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwa a ranar Alhamis cewa Mr. Ibrahim Khalil Gaga ya zama darekta a bankin shige da ficen kayayyaki.
Mai taimakawa shugaban Najeriyan ya fitar da jawabi cewa Ibrahim Gaga ya shafe sama da shekaru 25 yana aikin banki da shari’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin zamansa Darekta, Gaga shi ne Sakatare kuma mai bada shawara kan harkokin shari’a a majalisar da ke sa ido kan aikin NEXIM.
NEXIM: Karatun Ibrahim Khalil Gaga
Gaga yi digirinsa a jami’ar Bayero a Kano a kan ilmin shari’a, daga nan sai ya samu shaidar BL daga makarantar koyon aikin shari’a.
A shekarar 2022, Ngelale ya ce Gaga ya je jami’ar jihar Legas da ke Ojo, ya samu digigir, kuma yana da shaidar PGD daga NOUN.
Bayan gama karatun shari’a, Gaga ya fara aiki da kamfanin Ikiebe & Co a garin Legas.
Aikin banki kafin shigowa gwamnati
A lokacin da ya koma banki, ya yi aiki a Liberty Bank Plc, Pacific Bank Limited, MBC International Bank Limited, da First Bank.
Rahoton ta Leadership ta fitar ya ce sabon darektan ya taba aiki da bankunan Fidelity Bank Plc da irinsu ASO Savings & Loans Plc.
Tarihin bankin NEXIM a Najeriya
A shekarar 1991 aka kafa bankin NEXIM, lokacin Janar Ibrahim Badamasi yana mulki da nufin a bunkasa tattalin arzikin kasa.
Nairametrics ta ce aikin bankin sun bada bada dama ga masu sha’awa su shigo da kaya daga kasashen ketare ko su fita da su.
Kwamitin Oronsaye zai iya shanye NEXIM
Kuna da labari ICRC za ta koma karkashin BPP kamar yadda NCAA da wasu takwarorinta za su dunkule a gwamnatin tarayya.
Kwamitin Stephen Oronsaye ya bada shawarar soke hukumomin kula da alhazai, sannan NIPC da NEPC za su hadu duk a wuri guda.
Asali: Legit.ng